Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (3)

Daga AISHA ASAS

A wannan satin muke son kai ƙarshen wannan darasin na mu da muka shafe sati biyu muna kawo wa masu karatu, kuma idan har kuna biye da mu, mun faro ne da gabatar da ita kanta matsalar ta kogon haƙora, yadda ta ke samuwa zuwa dalilin yawaitar ta, ba mu tsaya ko’ina ba sai a wasu daga cikin hanyoyin da za a iya magance matsalar cikin sauƙi. A wannan satin ma dai za mu kawo wata hanyar ce da ta sha banban da waɗanda muka kawo a baya.

  1. Amfani da man kwakwa:

Man kwakwa na da ƙarfi matuƙa wurin magance matsalolin haƙora da yawa, kamar matsalar dasashi da ke sa zubar jini, warin baki, kogon haqora da sauransu. Don haka amfani da shi zai iya kawo ma ki lafiyar haƙora ta ɓangarori da dama.

Yadda za ki yi amfani da shi kuwa, shine, za ki ɗibi cokali ɗaya na man, ki zuba shi a bakinki, sai ki sa ɗan yatsa ɗaya kina juya shi har ya shiga inda matsalar ta ke sosai. Za ki karkata kanki a ɓangaren don ba shi damar game ko’ina. Wannan zai tsaya a bakin tsayin mintuna 21 kafin a wanke da ruwan ɗumi.

Zai iya qarawa wannan haɗin ƙarfi idan ya kasance ruwan ɗumin an ɗan saka masu gishiri ko kaɗan ne. kuma a guje haɗiye man bayan ya gama aikinsa. Kuma ga masu olsa ya kamata su yi taka-tsan-tsan da haɗiye haɗin don kasancewarsa ɗaya daga cikin ababen da ka iya tado da olsar.

Kuma wannan haɗin an so a yi amfani da shi ne da zaranan tashi daga barci, bayan kuskure baki da ruwa (kamar yadda muka sani, an so a jinkirta jin buroshi bayan tashi daga barci har sai an ɗan ci wani abu, saboda zai iya cutar da dasashi, kasancewar an yi na dare, wanda idan har an yi shi yadda ya kamata, to an kawar da duk wani datti da aka wanke bakin domin sa, hakan zai sa a tashi da safe ba tare da wata matsala ba.

Sai dai akan wanke bakin da ruwa kawai, don farkar da shi bayan jimawa da ya yi a rufe, kuma akwai waɗanda ke da matsalar tara yawu a baki wanda wannan wankin zai ba wa bakin damar iya shan wani abu ba tare da ƙyanƙyami ba.

An so a sha ko da ruwan shayi ne kafin a wanke baki da buroshi. Wannan haɗin kuwa za a yi amfani da shi ne da zaran an ɗauraye bakin, kafin a ci wani abu). Ana gabatar da wannan maganin ne sau ɗaya a rana.

Idan an jarraba waɗannan hanyoyin da muka kawo tun a sati biyu ba, kuma ba a samu sauƙi ba, to a hanzarta zuwa asibiti don sanin dalili.