Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Aunty Asas ina wuni. Ya aiki. Dan Allah ki taimaka min da shawarar yadda zan yi. Wallahi Ina son in yi aure, sai dai na kasa samun irin mijin da na ke so. Ina son kyakyawan namiji da tun a ganin farko zai kamu da matsananciyar soyayyata. Mu yi soyayya da za ta burge duk wanda ya gan mu. Ya zamana ba wanda zai kula sai ni kaɗai. Irin ko faɗa muka yi har jikinshi ya nuna yana cikin damuwa. Mai kuɗi da yawa, wanda ya iya girki don idan ba ni da lafiya. Wanda ba zai iya haɗa soyayyata da ta kowa ba koda iyaye ne. Dan Allah ki taimakamin da hanyar da zan samu irin wannan miji.

AMSA:

Lafiya lau. Alhamdu lillah. Irin mijin da kika zayyana ban san ta inda zan samo ma ki irinsa ba, bare har in sanar da ke hanyar da za ki bi zuwa gare shi. Sai dai idan zan tambayar miki marubuciya Saliha Abubakar Zaria, ko Jamila Uwar Tanko, ko K.Mashi, Antyn KD ko kuma Fatima Ɗan Barno su taimaka su aura miki ɗaya daga cikin jaruman littafansu.

Domin ita ce hanya ƙwaya ɗaya da na sani za a iya samun irin wannan miji. Domin mijin littafi na ji kin zayyano. Sai dai kafin komai ya kamata ki fara da tambayar kanki, shin ke matar littafi ce?

Irin matar da ke son mijinta fiye da komai, ta yi masa wanka, girki mai daɗi da ƙamshinsa zai karaɗe ko’ina, ta ba shi haƙuri idan ya yi mata laifi, ta kuma ba shi haƙuri idan ta yi masa laifi, mai ilimi, haƙuri, tarbiyya da matsananciyar tsafta. Wadda ta iya tarairiyar miji da danginsa tare da haƙuri da cin mutuncin mahaifiyarsa.

Matar da idan mijinta ya nemi ƙarin aure za ta taimaka masa, ta amshi amaryar da hannu biyu har ma ta ba su aron gadon ɗakinta a daren farko, sakamakon ba a gama yi wa amarya jere ba.

Idan har kuwa kina cikin wannan layi, zan iya cewa, ki zauna ki jiraye zuwan irin naki mijin. Idan kin san ba ki cika waɗannan hallaya ba, to ya kamata ki gaya wa kanki gaskiya cewa, ba ki cancanci irin mijin da kika zayyana ba.

Abu na gaba, zan so in janyo hankalinki kan sha’ani na aure, soyayya ba ita ce zaman aure ba, ban yi mamaki ba don kin ba ta babban matsayi ba, kasancewar ba ki shiga rayuwar auren ba. Kafin aure soyayya ta ke zama ginshiƙi na zamantakewa, amma da zaran kin zama matar aure, kuka yi zama na marmari, zuwa ‘yan shekaru halayyarku ce za ta ja ragamar rayuwar.

Wannan ne dalilin da ke sa kiga masoyan da suka yi soyayya tamkar za su mayar da juna cikinsu don so, amma ɗan lokaci bayan auren sai su zama maqiyan juna. A nemi soyayyar sama da ƙasa a rasa.

Zancen kyau da kika yi, abu ne sananne cewa, a lokacin da kuka yi aure, alaƙar kwanciya ta shiga tsakaninku na tsayin lokaci, to fa za ku kai lokacin da za ku daina ganin kyawon juna, saboda komai ya bayyana. Don haka matsanancin kyau bai kamata ya shigo jerin manyan abin dubawa yayin zaɓen mijin aure.

Ga duk wata da ke fatan zaman aure mai ɗorewa, to fa miji nagari ta ke addu’an samu, ko wane iri ne dai Allah ya yi mata zaɓi na ƙwarai. Domin idan kin samu miji na ƙwarai, za ki yi rayuwar aure cikin shauƙi da rashin gundura.

Shawarar da zan ba ki, ki ajiye wannan burin naki na hangen nesa, ki kalla a daidai ke, cikin manemanki ki zaɓo mai ɗan dama-dama wanda zuciyarki ta aminta da shi ko ba sosai ba, domin sau da yawa dawamammen so na ginuwa ne bayan aure, ta sanadiyyar kyautata wa juna. Ki ba wa Allah zaɓi ta hanyar yin addu’ar neman zaɓi da Manzon rahma ya koyar da mu.

Ki rabu da mijin littafi can cikin littafan soyayya, ki fuskanci gaskiya. Babu waɗanda suka fi sa’ar mazan aure na daga mata face waɗanda suka samu maza nagari.