Masu ruwa da tsaki a Bankin Sterling sun amince da sauya wa bankin suna

Daga AMINA YUSUF ALI

Bankin Sterling zai sauya suna bayan Sahalewar masu ruwa da tsaki.

A yanzu haka sunan bankin kaɗai wanda aka sani da bankin ba da rance zai sauya i zuwa shugaban rukunin bankunan hada-hadar kuɗi.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin mahukuntan bankin. Inda aka bayyana hakan ranar Litinin ɗin da ta gabata. Inda aka ƙara da cewa, yanzu kawai takardar amincewar masu ruwa da tsakin bankin kawai ake jira don zartar da wancan hukuncin.

A cewar su, bankin zai samu iko a kan kamfanonin da yake da hannayen jarinsa a ciki.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan mako guda da bankin ya yi ganawar bai-ɗaya da dukkan masu ruwa da tsaki a matsayin cika ɗaya daga sharuɗɗan kotu kafin a sauya tsarin bankin.

Sanarwar ta bayyana cewa, bayan an cimma matsaya, bankin zai tashi daga Sterling Banki zuwa Kamfanin Sterling Financial Holdings Company.

Wannan zai ba wa bankin iko da damarmaki wanda sauran bankuna masu irin lasisinsa ba za su iya samu ba. Sannan ya goga da sauran kamfanonin hada-hadar kuɗin wajen samun kuɗin shiga.

Rahotanni sun rawaito da cewa, da ma da irin wannan tsarin Bankin Stanbic IBTC ya kai matsayin da ya cimma a yanzu. Domin yana daga bankuna da suka fara kuma suke cin moroyar abin.