Rasuwar Sha’awa: FIDA da ƙungiyoyi 20 za su ɗaukaka ƙara – Barista Bilkisu

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Ƙungiyar Lauyoyi Mata (FIDA), ƙarƙashin jagorancin Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman, da wasu ƙungiyoyin jin ƙai 20 sun sha alwashin bin digdigi da haƙƙi na ganin an tabbatar da adalci ta hanyar shari’a kan duk wanda aka samu da laifin a rasuwar Sha’awa Abdullahi mai juna biyu da ta rasa ranta a Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Marigayiyar ta rasu ne sakamakon sakaci da rashin kayan aiki a lokacin da ta ke buƙatar kulawa gaggawa yayin da ta ke naƙudar haiwuwa a asibitin don neman taimakon jami`an lafiyar asibitin, kamar yadda yar uwarta Zainab Abdullahi ta yi zargin Asibitin ta yin sakaki tun ranar da su ka kai ’yar uwarsu Asibitin har kwana uku bata samu kulawar da ta kamata ba.

Barista Bilkisu, ta bayyana haka ne a lokaci wani taron ganawa na ƙungiyoyi jin qai da su ka goyawa ƙungiyar lauyoyi mata ta ƙasa reshan Jihar Kano baya kan wannan gwagwarmaya da fafutuka ta tabbatar da haƙƙin wanda aka zalinta bisa gagganci ko nuna halin ko-in-kula a kowani lokaci.

Ta ce, ganin yadda ɗaya daga cikin manyan lauyoyi kuma shugaba a wannan tafiya ta lauyoyi na cikin wannan gwagwarmaya ta neman haƙƙin Sha’awa Abdulmumini, su a matsayinsu na lauyoyi mata da sauran ’yan gwagwarmayar neman ’yancin al’umma to ba shakka idan aka je kotu kan wannan batu to su fa babban lauya kuma shugaba Mahmud, za su marawa baya na ganin an ƙwato wannan ’yanci na wannan baiwar Allah da ta kwanta dama.

Wakilimu da ya halarci wannan taro, ya rawaito mana cewa, wakilan ƙungiyoyi da dama ne su ka halarci wannan taro da FIDA ta shirya a ranar Asabar da ta gabata a Kano, kaɗai daga ciki akwai wakilan kafafan yaɗa labarai da shugaban hukumar kare haƙƙin bil adama na Kano, Shehu Abdullahi da mataimakin shugaban lauyoyi na ƙasa reshan jihar Kano NBA da sauransu.

Sai dai shi ma a hira sa da wata kafar yaɗa labarai, Babban Darkta DG na hukumar kula da Asibitoci na jihar Kano Dakta Sulaiman Hamza Mudi, ya shaida wa duniya cewa, a ƙoƙarin da hukumar kula da asbitoci ta jihar Kano, ta ke yi yanzu haka an ɗau matakin sallama ko kuma dakatarwa da ɗaukacin ma’aikatan asibitin da su ka yi aiki a wannan ranar a Asbitin Murtala domin tabbatar da adalci na yin bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da wani laifi na sakaci a wannan al’amari, da kuma tsame wanda ba shi da laifi a wannan abu mara daɗi da ya faru.

Shi ma wani ɗan jarida mai suna Haruna Galadanci, wanda na ɗaya daga cikin ’yan jaridun da su ka halarci taron FIDA ya ce, ya daɗe yana bin wannan lamari tun daga faruwarsa domin ya je har sau 13 kullum amsa iri ɗaya ce an kafa kwamiti kan lamarin. Kuma shi ma ya taɓa karo da matsala mai kama da wannan a harkar lafiya kan wani ɗan uwansa da ya rasu.