Kar ku katse zumunci a tsakaninku, Maikuɗi Dogo ga al’ummar Tafa

Daga MUHAMMAD ALI a Tafa

Shugaban Ƙungiyar Zumunta da Taimakon Jama’a, wadda ake ‘Community Development Association’ a Turance, da ta ke garin Tafa ta ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, Alhaji Maikuɗi Dogo, ya yi kira ga al’ummar garin, da kada su sare wajen cigaba da zumunci da zamantakewar da aka sansu da shi shekara da shekaru a tsakaninsu.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke hira da manema labarai yayin gudanar da babban bikinsu na Ajo da suka saba shiryawa akai-akai a harabar ƙungiyar da ke garin na Tafa a ƙarshen mako, inda ya yi nuni da cewa, sada zumunci da taimakon juna da al’umma baki ɗaya, sune makasudin kafa ƙungiyar.

Ya ce, yau shekara sama da 20 kenan da suka kafa aungiyar, a lokacin da membobi 60 kacal, amma yanzu, membobin ƙungiyar sun haura mutum 200 maza da mata da matasa waɗanda suka fito daga jihohi daban-daban na faɗin ƙasar nan, yana mai cewa, “Alhamdu Lillahi, ƙungiyar cikin shekarun nan, ta tallafawa membobin ta da dama ta hanyoyi daban-daban, kamar taimako wajen ɗaurin aure, marasa lafiya, jarin yin kasuwanci da sauransu “.

Alhaji Maikuɗi sai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta waiwaye su, ta taimakawa ƙungiyar da irin tallafin da ta ke baiwa ƙungiyoyi a Jihar, saboda gagarumin taimakon da ta ke yiwa jama’a musamman marasa galihu, da kuma hobbasar da ta ke yi wajen haɗa kai da jamai’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Tafa.

Sai ya gode wa Jami’an tsaron yankin akan goyon bayan da suke baiwa ƙungiyar, yana kuma jinjinawa shugabannin ƙungiyar da suke ci gaba da taimakon ƙungiyar da duk membobinta ta fannoni daban-daban, yana mai ƙarawa da cewa, burinsu a ƙungiyar, suga sun kafa muhimman abubuwa da za su ƙarawa ƙungiyar ƙaimi da cigaban membobinta.

Shugaban sai ya yi kira ga duk membobin da suka amfana da taimakon ƙungiyar, su yi amfani da duk abin da suka amfana dashi ta hanyar da ta dace, kuma su ci gaba da baiwa ƙungiyar goyon baya da haɗin kai, su kuma cigaba da zama masu bin doka da oda.

A na shi ɓangaren, Uban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Rilwanu Jarma, ya yi karin bayani a kan irin taimakon da ƙungiyar ta yi kuma tana ta yiwa membobinta, yana mai cewa, sanadin taimakon ƙungiyar, wasu dayawa sun sayi gidaje, wasu sunje Makka, wasu an ba su jarin yin kasuwanci ko bunƙasa sana’arsu, wasu kuma an Tallafa musu wajen yin aure, haka matasa, da yawa ƙungiyar ta ɗauki nauyin karatunsu, wasu kuma an samar musu aiki da jarin yin sana’a, da sauransu.

Kuma har yanzu, ƙungiyar na ci gaba da abin da ta saba yi, wato taimakon jama’a. Sai ya gode wa jami’an tsaro a kan goyon bayan da suke basu cikin tsawon shekaru 20 da kafa ƙungiyar, musamman DPO na yankin.

Alhaji Rilwanu ya yi takaici a kan yadda har yau, ba su amfana da abin da ya kira ‘romon dimokaraɗiyya’ ba, don haka, ya kai kukan shi a madadin ƙungiyar, ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, da ya “dube mu da idon Rahama, ya tallafa mana saboda tasirin ƙungiyar a tsakanin al’ummah da zaman lafiyar da muka gina a cikin garin Tafa bisa ikon Allah, babu faɗa, babu tashin hankali.”

A tasu gudunmawar, mataimakin ƙungiyar, Alhaji Haladu Musa Usman da kakakin ƙungiyar (PRO) Alhaji Salisu Hassan, duk kira sukayi ga Gwamnati da ta tallafawa ƙungiyar saboda taimakon jama’a da take ta yi shekara da shekaru.

Ita ma Shugabar mata, Hajiya Ladidi Kabuga, kira ta yi ga membobin ƙungiyar, maza da mata, da suci gaba da bin dokokin ƙungiyar, su kuma zama masu ladabi da biyayya, har ila yau, su kasance masu Kyakkyawar zamantakewa a tsakaninsu.

An dai tashi bikin lami lafiya. Cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai Alhaji Danladi Obajana, Alhaji Baffa na ‘yan Canji, Alhaji Musa mai Shadda, Alhaji Abubakar mai Dubu-Dubu, Alhaji Wawan Sarki, Hakimi Uban Badodo daga Bauchi, da Alhaji Dilan fata daga Gombe. Wasu kuma sune, Hajiya Maimuna kawo daga Kano; Hajiya Maryam Oka. Jamila Gombe; Hajiya Jummai daga Mokwa, da Hajiya Fati Cestelo daga Mararrabar Jos.

Sauran sun haɗa da Usaina daga Mararrabar Jos, Hajiya Bilki daga Kano, da kuma Hajiya Aisha daga Bauchi.