2023: An fara kamfen

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Doguwar dimokuraɗiyyar Nijeriya ta shiga shekara ta 24 bana daga fara ta a 1999. Bayan dogon mulkin soja an samu nasarar komawa tafarkin dimokuraɗiyya a Nijeriya inda tun a na fargabar za a samu dawowar sojoji har ta kai ga ’yan siyasa yanzu sun warware kafa su na mulkin su bisa tsarin mulki da ya raba turakun gwamnati su ka zama uku wato sasahen zartarwa, majalisa da kuma sashen shari’a. Jamhuriya ta farko ta yi kimanin shekara 6 ne inda sojoji su ka yi juyin mulkin da su ka zubar da jinin farar hula a 1966.

Ba a sake samun dawowa dimokurɗiyya ba tun lokacin sai a 1979 inda a ka yi zaɓe marigayi Alhaji Shehu Shagari ya lashe zaɓe a inuwar jam’iyyar NPN mai alamar MASARA a jamhuriya ta biyu kenan.

Shagari ya yi nasarar kammala wa’adin mulkinsa na farko har ya sake lashe zaɓe a wa’adi na biyu a 1983 amma sai sojoji su ka dawo su ka kifar da gwamnatin. Allah ya sa an ɗan samu bambancin dawowar sojojin a wannan karo inda ba su zubar da jinin shugaban ƙasa ba kamar yanda su ka yi wa Firaminista Tafawa Balewa, marigayi Firimiya Ahmadu Bello da Ladoke Akintola.

Kazalika a lokacin an samu sauyi daga mulki na tsarin Birtaniya mai shugaban ƙasa da Firaminista zuwa tsarin Amurka mai shugaba mai cikekken iko. Tun daga nan ba a sake nasarar dawowa cikakkiyar dimokuraɗiyya ba sai a 1999 don ko zaven watan Yunin 1993 bai kai labari ba.

Wannan sabuwar tafiya da mu ke magana ta zama mai tsawo a tarihin Nijeriya da kuma kasancewar an samu miƙa mulki tsakanin gwamnatocin farar hula kuma aƙalla an samu jam’iyyu biyu sun dare karaga da su ka haɗa da PDP da kuma APC duk da gamayyar jam’iyyun hamayya ne su ka kafa ta.

Za a jira yanzu a ga wace jam’iyya ce za ta hau karagar mulki a zaɓen 2023. Haƙiƙa an yi shauƙin dawowar ’yan siyasa bayan dogon mulkin soja kuma a ka sake son jam’iyyar gwamnati daga 1999-2015 wato PDP ta sauka don samun sabuwar tafiya.

Gajiyawar akasarin jama’a ta kai ga har wasu na yin tamkar mutum-mutumi su lulluve da tutar PDP su ce sun yi jana’izar jam’iyyar. Hakanan wasu kan jirkita musamman hoton tsohon shugaba Jonathan su maida shi wata shagga mai shan jini don nuna kin jinin su ga mulkin PDP.

Ba wani mamaki an yi murna ainun da samun shigowar ‘yan adawa gwamnati a 2015 don tunanin cewa su na talakawa kuma za su gyara lamuran da su ka taɓarɓare a ƙasar kama daga ƙuncin tattalin arziki, ƙalubalen tsaro, rashin magunguna a asibiti, taɓarɓarewar makarantu, cin hanci da rashwa, zaman kashe wando da sauarn su.

A yau da sabuwar gwamnatin tsoffin ’yan hamayya ke cika shekaru 8 kan gado an samu mutane da daman a nuna gajiyawarsu da gwamnatin da ma dawowa daga rakiyar ’yan siyasa. Ko da dai an samu sauyin fuskokin masu mulki na yanzu, amma ba lalle ne komai a ce ya gyaru ba.

In an ci ansarar karya lagon ’yan boko haram, yau an wayi gari an samu barayin mutane da kuma masu zubar da jinin wadanda su ke jin haushi da sunan gwagwarmayar kafa ƙasar Biyafara. Ko da za a ce an samu sabbin waɗanda su ka samu kuɗi amma da yawa talakawa sun ƙara shiga ƙuncin rayuwa ne.

Matsalolin sun ƙara ta’azzara ne daga yadda a ka tava samun koma bayan darajar sayar da fetur da kuma annobar da ta yi wa tattalin arzikin duniya illa mai yawa. Ko da mutum zai ce APC ba ta tavuka abun kirki ba, sai ya ƙara dubawa zai ga wasu manya a gwamnatin tsoffin ’yan PDP ne.

Ko da ma yunƙurin da a ke yi na kafa jam’iyyu ta uku mafi ƙarfi za a tarar akwai waɗanda su ka fice wa imma daga PDP ko APC su ka fada can don ƙorafin ba a yi mu su adalci ba. Har yanzu dimokuraɗiyyar Nijeriya ba ta kai yadda masu rinjaye a jam’iyya za su cigaba da zama a jam’iyyarsu ko da ta faɗi zaɓe.

Abun takaici ma wasu masu zaunawa a jam’iyyun kan ɗauka su ke da gadon jam’iyya kuma duk wanda ya shigo sai dai ya zama ya na ƙarƙashin su ko kuma ya yi gaba. Kazalika a yau ba jam’iyyar da ta tsira daga sauya sunan ’yan takara da wasu ’yan lele.

Koyaushe za a samu wasu na kuka wasu na dariya. Don haka ba a kai ga lokacin da za a wayi gari kowa ya na da ’yanci ya samu abun da ya nemi bisa ƙa’ida ba.

In mun sake dubawa za mu ga daɗewar sojoji kan mulki ya sa wasu daga cikinsu na marmarin in sun yi ritaya sai su dawo su shiga siyasa har ma ka ga an zave su da kayar da waɗanda su ka tashi duk rayuwar su siyasarsu ke yi.

Tun sanyin safiyar wannan dimokuraɗiyya a ka zaɓi tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya Olusegun Obasanjo ya zauna kan mulki na tsawon wa’adi biyu a shekaru 8 inda har ma don zakin mulkin ya so ya zarce a karo na uku.

A duk mulkin Obasanjo babban mai adawa da shi shi ne tsohon shugaban mulkin soja Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya). Shugaba Buhari wanda a shekarun baya, ba ya sha’awar lamuran siyasa ya tsinci kansa tsundum a siyasar biyo bayan neman ya yi hakan da wasu aminan sa su ka yi ma sa.

Don haka ya nuna tun da dimokuraɗiyyar za ta cika shekaru 24 cif a baɗi, tsoffin shuagabannin mulkin soja sun share biyu bisa uku na adadin shekarun a karagar mulkin babbar fadar Aso Rock.

Shin tsoffin sojojin sun dace da yanayin dimokuraɗiyya ko kuwa a’a ba abun da za a iya yi don tsarin mulki ya ba su damar ysayawa zaɓe kuma a zaɓe su. A fa wannan dimokuraɗiyyar ce a ka samu tsohon soja ya jagoranci ginshikin dimokuraɗiyyar wato majalisar dattawa wato David Mark wanda ya zauna kan kujerar tun 2007-2015, kazalika ya cigaba da zama ɗan majalisar dattawa daga mazaɓar Arewa maso gabashin jihar Binuwai har 2019 kafin tsohon ministan cikin gida Abba Moro ya hau kujerar.

Har yanzu haka siyasar ke tafiya shinkafa da wake har ma da tsakuwa. Mafarkin da a ke yi ya zama an wayi gari da zaɓar masu kishin ƙasa har zuci su shuagbanci babbar ƙasar mafi yawan baƙar fata a duniya da za su iya aiki cikin adalci ta hanyar magance bambancin ƙabilanci, yanki da sauran dalilai da kan raba kan ƙasa.

A tarihin dimokuraɗiyya a Nijeriya an samu shugabanni a kowane ɓangare da za su iya sadaukar da ran su don cimma burin waɗanda su ka zaɓe su. A zamanin yau sai ɗaiɗaiku da kan tuna jama’a masu zaɓe fiye da abun da za su cika aljifansu da shi.

Duk da buɗe damar fara kamfen da hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta yi, ’yan takarar manyan jam’iyyu da ke alwashin shiryawa tsaf don tinkarar zaɓen; ba su ƙaddamar da kamfen ba a ranar larabar 28 ga satumba 2022.

A zahiri dalilan hakan sun saɓa da na yadda a ka saba na logar jiran wata jam’iyya ta fara kamfen ɗin don zama damar gano logar ta ga abokiyar hamayya.

In za a tuna a zaɓen 2019, APC ta caccaki ɗan takarar PDP Atiku da cewa ya na son sayar da Nijeriya ga abokan sa ta hanyar cewa in an zaɓe shi zai sayar da jarin kamfanin fetur na NNPC.

A wannan karo APC na bayyana cewa ta na son faɗaɗa sunayen jami’an kamfen ne ba tare da ambatar labarin fita ƙetare da ɗan takarar ta Bola Tinubu ya yi ba.

Kamfen ɗin APC ta bakin jigon tafiyar Ibrahim Masari na nuna in APC ta zarce za ta sakawa waɗanda su ka yi ma ta hidima da hakan sauyi ne daga yadda gwamnatin Buhari ta ke tafiya a halin yanzu.

A ɓangaren Atiku Abubakar na PDP wanda ya na Inugu ‘yan sana’o’i gabanin sanarwar dakatar da ƙaddamar da kamfen a Abuja ya fi maida hankali ne wajen shawo kan yankin Ibo da tsohon mataimakin takararsa Peter Obi ya fito kuma ya tsaya yanzu takara a jam’iyyar LEBA.

Hakanan don qiqi-ƙaƙa tsakanin sa da gwamnan Ribas Nyesom Wike, ya qarfafa hulɗa da tsaohon shugaban jam’iyyar Uche Secondus daga Ribas ɗin don rage kaifin illar da hakan zai jawo ma sa.

Rabi’u Kwankwaso na NNPP na cigaba da taruka ne da ’yan jam’iyyarsa don ƙara ƙarfafa tasirin ta inda har jigon ta Buba Galadima ke cewa in har Kwankwaso bai lashe zaɓe kai tsaye ba za a iya kai wa zagaye na biyu.

Kwankwaso dai kullum kan ce ya san ƙabli da ba’adin takarar siyasa.

Kammalawa;

Hukumar zave ta bakin jami’ar labaru Zainab Aminu na cewa yanzu kamfen ɗin gwamnoni ne da majalisar jiha ke zuwa a ranar 12 ga Oktoba 2022.

Tun zaɓen 2007 inda Obasanjo ya sauka don ƙarewar wa’adi bayan gaza tazarce karo na uku; sai a 2023 in Allah ya hukunta ne za a maimaita zaɓe ba tare da shugaba da ke kan gado ya na jerin ’yan takara ba.