Wasu shugabannin Afirka sun taya Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin murnar cika shekaru 73 da kafuwa

Daga CMG HAUSA

A baya-bayan nan, shugabannin ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama ne, suka bugu waya ko aiko da wasiƙu ga Xi Jinping, babban sakataren kwamitin ƙolin JKS, kuma shugaban jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, don taya murnar cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, tare da fatan samun nasarar gudanar da babban taron wakilan JKS karo 20 dake tafe.

A saƙonsa, shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi fatan babban taron wakilan JKS karo na 20, wanda ke da ma’ana a tarihi, zai gudana cikin nasara.

Ya kuma bayyana cewa, yana fatan taron zai fito da wani tsari na ci gaban ƙasar Sin a nan gaba.

Ya ƙara da cewa, Najeriya na son ƙarfafa cuɗanya da haɗin gwiwa da ƙasar Sin, da ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin ƙasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Shi ma shugaban ƙasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana cewa, ƙasar Sin ƙasa ce mai da’awar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, da cuɗanyar bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaito a duniya.

Ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta ƙuduri aniyar tallafawa ci gaban ƙasashen Afitrka baki ɗaya.

Shugaba Akufo-Addo, ya bayyana cewa, ƙasarsa na fatan sassan biyu, za su inganta haɗin gwiwa a tsakaninsu da haɗin gwiwar ɓangarorin daban-daban, da ƙarfafa dankon zumunci a tsakanin al’ummominsu, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga ɗaukacin bil-Adama.

A madadin gwamnatin da jama’ar ƙasar Afirka ta Kudu kuwa shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa, ya mika gaisuwa da taya murna ga shugaba Xi da gwamnati da jama’ar ƙasar Sin, yana mai jaddada cewa, ƙasarsa a shirye take ta ƙara ƙarfafa zumunci da abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin ta da ƙasar Sin.

Mai fassara: Ibrahim Yaya