Ƙasashen duniya sun nuna goyon baya ga shawarar samun bunkasuwar duniya

Daga CMG HAUSA

A watan Satumba na shekarar 2021, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarar samun bunƙasuwar duniya bisa taken “yadda za a samu bunƙasuwar duniya da salon bunƙasuwar da ake fatan samu a duniya”.

A cikin sama da shekara ɗaya, ƙasa da ƙasa sun nuna goyon baya ga wannan shawara.

Ya zuwa yanzu, ƙasashe fiye da 100 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama ciki har da MƊD, sun nuna goyon baya ga shawarar, kana ƙasashe fiye da 60 sun shiga rukunin haɗin gwiwa na raya shawarar samun bunƙasuwar duniya.

Babban sakataren MƊD António Guterres ya nuna yabo ga ƙasar Sin kan muhimmiyar rawar da ta taka wajen goyon bayan ra’ayin ɓangarori daban daban, da sa ƙaimi ga yin haɗin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa, da samun bunƙasuwa mai ɗorewa.

MƊD ta nuna goyon baya ga shawarar raya duniya, tana mai imanin cewa, shawarar za ta taimaka wajen raya ajandar samun bunƙasuwa mai ɗorewa nan da shekarar 2030.

Tsohon firaministan ƙasar Togo kuma shugaban asusun raya aikin noma na ƙasa da ƙasa Gilbert Houngbo ya yi nuni da cewa, asusun ya yaba da aikin yaƙi da talauci, da tabbatar da samun isasshen abinci, da samar da kuɗaɗe domin samun bunƙasuwa, da samun ci gaba ba tare da gurɓata muhalli ba da sauransu da aka sanya cikin shawarar samun bunƙasuwar duniya.

Kana yana fatan bisa shawarar da burin samun bunƙasuwa mai dorewa, ƙasashen duniya da yankuna za su gudanar da shawarwari da haɗin gwiwa mafi dacewa.

Mai fassara: Zainab