Ya kamata a koyi fasahohin raya demokuraɗiyya na Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jama’ar ƙasar Kamaru Theodore Datouo ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya cewa, demukuraɗiyya ta sha bamban da yanayin ƙasa da ƙasa, tsarin demokuraɗiyya na gurguzu na ƙasar Sin ya dace da yanayin ƙasar Sin, kana ya taimaka wajen samun ci gaba a ƙasar, don haka ya kamata a yi koyi da fasahohin ƙasar Sin a wannan fanni.

Datouo ya ce, akwai bambancin al’adu a tsakanin ƙasa da ƙasa, don haka demokuraɗiyya ma ta sha bamban, ya kamata kowace ƙasa ta raya demokuraɗiyya bisa yanayinta.

Datouo ya ƙara da cewa, yadda ake aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuraɗiyya na ƙasar Sin ya burge shi sosai, ta hanyar amfani da tsari mai dacewa, ana iya daidaita ayyukan yin zaɓe bisa demokuraɗiyya, da yin shawarwari, da ba da shawara, da sarrafa harkoki, da kuma sa ido.

Sin ta samu mutane da dama tare da yankuna masu faɗi, tsarin demokuraɗiyya yana bai wa jama’ar ƙasa, damar ba da shawara kan yadda za a tafiyar da harkokin ƙasa.

Hakazalika, ya ce, muddin raya tsarin tafiyar da harkokin ƙasa zai taimaka wajen samun ci gaba a ƙasa da kawo moriya ga jama’ar ƙasar.

A matsayinta na ƙasa mai tasowa mafi girma, Sin ta samu ci gaba cikin sauri, da samun nasarori a fannoni daban daban, kuma tsarin demokuraɗiyya na ƙasar Sin ne ya taimaka ga samun bunƙasuwar ƙasar.

Mai fassara: Zainab

By Editor