Tinubu: APC ta nesanta kanta da wasiƙar da ake zargin Adamu ya rubuta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Alhamis ne Jam’iyyar APC ta nesanta shugabanta, Sanata Abdullahi Adamu, daga buɗaɗɗiyar wasiƙar da ya ce ya rubutawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, inda ya zarge shi (Tinubu) da yin gaban kansa wajen fitar da sunayen ‘yan majalisar yaqin neman zaɓensa.

Jam’iyyar mai mulki ta ce wasiƙar ba ta fito daga shugabanta ba, kuma wasiƙar da ke yawo ba ta hannun Adamu ta fito ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya ƙaryata wasiƙar a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Alhamis.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, bayan mako guda da fitar da jerin sunayen ‘yan majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, Tinubu ya sha kakkausar suka daga shugabannin da kwamitin ƙoli na jam’iyyar na ƙasa.

A wata takarda da kakkausar murya da Adamu ya rubuta kuma ya sanya wa hannu ga Tinubu wanda har yanzu ya ke hutu a Landan, jam’iyyar ta zarge shi da nuna girman kai da yin watsi da gudunmawar da suka bayar na kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

Sai dai Morka ya ce wasiƙar ba ta sa hannu ba, don haka bai kamata a dangana ga shugaban jam’iyya mai mulki ba.

“An jawo hankalinmu ga wata takarda wacce ba ta ɗauke da sa hannun kowa da ake yaɗa wa cewa mai girma Sanata Abdullahi Adamu, shugaban babbar jam’iyyar mu ta ƙasa ya rubutawa mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar mu, cewa ya nuna rashin gamsuwa da jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban qiasa (PCC).

“A bayyane yake, wasiƙar ba sahihiya ba ce kuma ba ta fito daga jam’iyyar ba. Wasiƙar da ba a sanya hannu ba wacce ke nuna kanta a matsayin ba tabbatacciya ba ba za ta iya ba kuma bai kamata a dangana ta ga marubucin da aka zayyana ba.

“Shugaban jam’iyyarmu na ƙasa da ɗan takararmu na shugaban ƙasa suna da alaƙa mai kyau tsakanin su kuma su na aiki cikin aminci,” inji shi.