Ƙasashe 143 sun kaɗa ƙuri’ar yin tir da mamayar Rasha a Ukraine

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri’ar yin tir da Rasha kan mamaye wasu sassan Ukraine da ta yi, matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce saƙo ne mai ƙarfi ga takwaransa Vladmir Putin.

Ƙasashe 143 ne suka goyi bayan ƙudurin na yin tir da Rasha a zauren Majalisar Ɗinkin Duniyar, inda 5 suka hau kujerar na ƙi, sauran ƙasashe 35 kuma suka ƙauracewa zaman, wadanda suka haɗa da Chana, Indiya, Afirka ta Kudu da kuma Pakistan, duk da matsin lambar da Amurka ta riƙa musu kan su yi tir da Rashan.

Ƙudurin dai ya yi tir da matakin Rasha, na shirya zaɓen raba gardama a cikin iyakokin Ukraine da kuma yunƙurin mamaye yankuna huɗu na ƙasar ta ƙarfin tsiya da shugaba Vladimir Putin ya sanar a watan jiya.

Ko a watan Satumban da ya gabata, sai da majalisar ta nufaci kaɗa makamanciyar ƙuri’ar amma Rasha ta yi amfani da kujerarta wajen daƙile yunƙurin duk da matakin Amurka na kafiya don tabbatar da ganin an yi tir da Moscow.