Ƙasashen Larabawa sun soma tura agajin abinci da magunguna zuwa Afghanistan

Qatar ta ce ta soma gudanar da ayyukan bada agaji na ‘yan kwanaki ya zuwa Afghanistan inda za ta riƙa tura kayayyakin buƙata na yau da kullum don amfanin ‘yan ƙasar.

Qatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon jinkirin kai tallafi ƙasar da aka samu daga ɓangaren ƙasashen yammaci tun bayan da Taliban suka karɓe ikon ƙasar a watan jiya.

Qatar ta yi wannan yunƙuri ne bayan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Baharain suka tura kayan agaji zuwa Afghanistan a ƙarshen mako da suka haɗa da kayan abinci da kuma magunguna.

Bayanai sun nuna an ga jirgin Qatar ɗauke da kayan agaji ya sauka birnin Kabul a ranar Asabar, inda Jakadan Qatar a Afghanistan, Saeed bin Mubarak Al Khayareen ya tarbi kayan.

Kusan rabin al’ummar Afghanistan da yawansu ya kai milyan 40 ne, ciki har da ƙananan yara su milyan 10, ke buƙatar agaji tun farkon wannan shekarar kamar yadda bayanan hukumomi suka tabbatar.