Guinea: Mun kama Shugaba Conde mun rushe gwamnatinsa – Sojoji

Sojojin ƙasar Guinea sun yi iƙirarin cewar sun gudanar da juyin mulki sun kuma kama Shugaba Ƙasa Alpha Conde, yayin da a hannu guda gwamnati ke cewa ta daƙile yunƙurin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ya samu faifan bidiyo mai ɗauke da wani hafsan soji kewaye da wasu sojojin da ke ɗauke da bindigogi da yake sanar da kama shugaban ƙasa da kuma soke kundin tsarin mulkin ƙasar.

Hafsan sojin ya kuma sanar da rufe iyakokin sama da ƙasa da kuma rusa gwamnatin ƙasar, amma kuma gwamnatin Conde ta sanar da gabatar da sanarwar da ke bayyana murƙushe yunƙurin da sojojin suka kai Fadar Shugaban Ƙasa.

Rahotanni daga birnin Conakry sun tabbatar da jin ƙarar harbe-harbe da muggan makamai a kusa da Fadar Shugaban Ƙasar da ke Yankin Kaloum, yayin da mazauna yankin suka ce sojoji sun buƙace su da su koma cikin gidajen su.

Kanal Mamadi Doumbouya, shi ne wanda ya yi wa ‘yan ƙasa jawabi kan wannan danbarwar, kuma har ya kammala jawabinsa bai bayyana wa ‘yan ƙasar inda Shuga Conde yake ba.

Shugaba Conde ya soma fuskantar ƙalubale ne tun lokacin da ya bayyana kwaɗayinsa na meman shugabancin ƙasar karo na uku a bara.

Wani hoton bidiyo da aka yaɗa ya nuna inda aka ji sojojin ƙasar na cewa, “Mun yanke shawarar sauke kundin tsarin mulkin ƙasa bayan kama shugaban ƙasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *