Nijeriya ta yi tir da juyin mulkin Guinea

Gwamnatin Nijeriya ta yi tir da juyin mulkin da sojoji suka yi a Tarayyar Guinea ran Lahadi.

Nijeriya ta nuna damuwanta kan juyin mulkin ne cikin wata sanarwar manema labarai da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar, inda ta bayyana juyin mulkin da lamari da ya saɓa wa dokar Ƙungiyar ECOWAS kan sha’anin dimukuraɗiyya da kuma shugabanci nagari.

Nijeriya ta ce sam ba ta goyi bayan haka ba kuma ba za ta taɓa mara wa hakan baya ba.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar, Esther Sunsuwa, ta sanya wa hannu, Nijeriya ta yi kira ga waɗanda ke da hannu cikin wannan badaƙala da su gaggauta maida gwamnatin ƙasar zuwa tsarin da aka san ta a kai tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar.

A wannan Lahadin ne sojojin ƙasar Guinea suka yi iƙirarin cewa sun kama Shugaban Ƙasar, Alpha Conde, tare da kifar da gwamnatin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *