Ƙuncin Rayuwa: Gwamna Sule ya ƙaddamar da shirin bai wa talakawansa tallafi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A matsayin mataki na rage wa ‘yan jihar Nasarawa ƙuncin ratuwar da ake fuskanta a ƙasa, Gwamnan jihar, Abdullhi Sule, ya ƙaddamar da shirin ba da tallafi na musamma inda aka raba kayan abinci da kuɗi ga waɗanda suka samu cin gajiyar shirin.

Sule ya ƙaddamar da shirin a yankin rayawa na Azara da ke Ƙaramar Hukumar Awe a jihar, inda aka fara da buhun shinkafa 1,600 da kuɗi N5000 ga kowannensu.

An zaɓo waɗanda suka fara cin gajiyar shirin ne daga sassan yankin da suka haɗa da Akiri, Azara, Ribi da kuma Wuse.

An ƙaddamar da shirin a ranar Juma’a, wanda taron ƙaddamarwar ya samu mahalarta daga sassan jihar.

Gwamna Sule ya kuma yi amfani da wannan dama wajen duba aikin gyaran hanyar Azara da ke gudana.

By Editor