Gobe za a yi bikin cika shekaru 38 da kafa makarantar BMC a Kano 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A gobe Asabar ne Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Aikin Jarida ta Ƙasa wato Basic Mass Communication School Old Student Association (BAMCOSA) za ta yi taron cikar makarantar shekara 38 da kafuwa da kuma taron shekara-shekara da zai gudana a makarantar da ke Agency for Mass Education daura da makabartar Ɗandolo da ke G/Dutse, Kano.

Taron wanda shi ne karo na farko tun kafuwar makarantar, ana sa ran halartar Mataimakin Gwamnan Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo da Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da Kwamishinan Ilimi Alhaji Haruna Doguwa da kwamishinan yaɗa labarai, Baba Halilu Ɗantiye, da malaman makarantar na da da na yanzu da kuma dukkanin tsofaffin ɗalibai na kasa baki ɗaya.

Shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na ƙasa Comrade Ismaila Ammani Maizare, tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu NUJ na Jihar Kano kuma Majidaɗin Sarkin Shanun Kano, ya ce kakasudin shirya taron shi ne faɗakar da shugabanni da jama’a muhimmancin makarantar wajen kyankyashe ɗaruruwan kwararrun ‘yan jaridu a Kano da kasa baki ɗaya.

Comrade Maizare ya qara da cewa “Babban burinmu shi ne ɗaukaka darajar Makarantar (Affiliation with University) don fara gabatar da National Diploma in Mass Comm, Advanced Diploma, Advanced Certificate da kuma Professional Diploma.

“Sannan za mu kewaya da manyan baƙi filin da muke son ginawa don habakawa da karin ajijuwan makarantar don haƙiƙa sun yi kaɗan.”

Kazalika a yau Juma’a ne za a gabatar da wasan ƙwallon ƙafa da wannan ƙungiya ta tsofaffin ɗalibai ta BMC da kuma ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta jihar Kano, da ƙarfe 4 na yamma a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, inda ake sa ran halartar shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano wato Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan, kuma shugaban tsare-tsare na hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, da kwamishinoni da sauran manyan baki.

By Editor