Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba da ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen magance matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.
Dauda ya yi wannan yabon ne a ranar Juma’a kuma a wajen ƙaddamar da babban masallacin Birnin Magaji wanda Hon. Aminu Sanin Jaji ya gina a garin Birnin Magaji, hedikwatar ƙaramar hukumar Birnin Magaji.
Gwamnan ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta shiga tsakani kan matsalar rashin tsaro sakamakon ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
“Ina so in nemi agajin Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta tsoma baki cikin gaggawa kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jihata”.
Haka nan, ya yaba wa Hon. Aminu Sanin Jaji na gina babban masallacin Juma’a a garinsu.
Gwamna Dauda ya bayyana ƙoƙarin Hon. Aminu Sanin Jaji da cewar abin a yaba ne domin zai taimaka wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci a yankin.
Daga nan, ya yi kira ga sauran ‘yan majalisar tarayya da su yi koyi da shi a kan haka.
Da yake jawabi tun farko, Hon. Aminu Sanin Jaji mai wakiltar Birnin Magaji da Ƙaura Namoda a majalisar wakilai ta tarayya ya bayyana cewa aikin gina masallacin ya laƙume miliyoyin naira.
A cewarsa, ƙarin ayyukan raya kasa a fannonin kiwon lafiya, samar da ruwan sha, ilimi da dai sauransu na daga cikin abubuwan da ya sa a gaba don amfanin al’ummar mazaɓar.
