Zanga-zangar lumana za a yi ba ta tashin hankali ba – Martanin ‘yan ƙwadago ga DSS

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeirya ta ce babu gudu babu ja da baya kan zanga-zanagar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar.

’Yan ƙwadagon na martani ne ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa gargaɗin da ta yi cewa ƙungiyar ta dakatar da ƙudirin da ta gabatar na zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.

A baya dai hukumar ta shawarci ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC da takwararta ta TUC da su janye matakin da suka ɗauka, inda ta ce hakan zai tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Sai dai da yake mayar da martani kan gargaɗin na hukumar DSS, a wata sanarwa da ya fitar, shugaban ƙungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya ce bai kamata hukumar ta yi wa ƙungiyar barazana ba amma ta mayar da hankali kan kame waɗanda ke son yin amfani da damar zanga-zangar don haddasa rikici.

Shugaban ƙungiyar ƙwadagon, wanda ya bayyana matakin da ke tafe a matsayin “zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa”, ya ƙara da cewa ƙungiyar ba za ta naɗe hannunta ba yayin da ’yan Nijeriya ke cigaba da rayuwa cikin ƙunci.

Ya ce, “Mun damu da shawarwarin da jami’an tsaron ƙasar nan suka ba mu na cewa mu jingine batun gudanar da zanga-zangar da muka shirya yi kan tsadar rayuwa da ba a taɓa ganin irinta ba duk da irin wahalar da ƙasar nan ke fama da shi, da hauhawar farashin kayayyaki, da taɓarɓarewar darajar naira inda dalar Amurka ta kai N1,900’’.

Ya kuma ƙara da cewa, “A cewar hukumar, ya kamata a jingine zanga-zangar da aka shirya domin zaman lafiyar jama’a”, la’akari da cewa zanga-zangar na iya zama tashin hankali da rikici duk da cewa muna da tarihin gudanar da zanga-zangar lumana.

By Editor