Da Ɗumi-ɗumi: An tsige Shugaban Majalisar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

An tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon Bilyaminu Moriki, yayin da Hon. Bashar Gummi ya karɓi ragamar shugabancin majalisar.

Wakilin mu ya tattaro cewa, mambobi 18 cikin 24 sun amince da tsige shugaban majalisar a wani taron gaggawa da suka yi a daren Alhamis.

MANHAJA ta gano cewa tsigewar ba ta rasa nasaba da ƙudirin da ɗaya daga cikin mamba mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Maru, Hon. Nasiru Abdullahi ya kawo gaban majilisar yayin taron gaggawar da suka gudanar a jiya na buƙatar a cire shi.

Mambobi masu daraja za su iya zaɓar wanda zai zama kakakin majilisar bisa doka na wucin-gadi watau ‘Pro-Tempo’ a Turance, in ji shi.

Ta bakinsa, “Sunana Honorabul Nasiru Abdullahi Maru mai wakiltar mazaɓar Maru ta 1, na miƙe ne domin ra’ayin naɗa Bashar Gumi a matsayin kakakin majalisar na wucin-gadi.

“Sabon kakakin majalisa Hon. Bashar Gummi, masu girma ‘yan uwa, za mu fara da wani al’amari na gaggawa ga jama’a.”

Binciken da wakilin mu ya yi ya gano tsige Hon. Moriki a matsayin kakakin msjalisar ya biyo bayan sake ɓullar matsalar rashin tsaro sakamakon yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan al’umma a faɗin jihar.

An ce shugaban majalisar mai barin gado ya yi kwanaki ba shi a jihar kafin su tsige shi.

Hon. Shamsudeen Basko mai wakiltar Talata Mafara ya shaida wa sabon shugaban majalisar cewa, batun rashin tsaro na ɗaya daga cikin abin da ya kamata a ba shi fifiko wanda ya kai ga tsige shugaban majalisar.

“Ina da batutuwa guda biyu amma an yi nazari a kan ɗaya, wato na rashin tsaro da ke damun jama’armu, ana kashe wasu, ana kuma sace su.

“Ban san abun da muke yi a majalisa ba, ya kamata mu tashi mu yi wani abu don kare jama’armu saboda ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a hedikwatar ƙananan hukumomin ba tare da ƙalubalantarsu ba,” in ji Hon. Basko.

Ya ƙara da cewa, “Muna kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki a yanzu don kare al’ummarmu.”

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa gwamna Dauda Lawal ya shafe sama da mako guda baya jihar har zuwa lokacin da aka tsige kakakin majalisar.