Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar, kan ƙarin kashi 50% da aka yi wa kuɗin sadarwa, wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi kwanan nan. Wannan mataki ya biyo bayan wata tattaunawa da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnatin tarayya da aka gudanar da yammacin Litinin.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana wa manema labarai bayan ganawar cewa gwamnati ta amince da kafa wani kwamiti mai faɗi domin duba tsarin ƙarin kuɗin sadarwa gaba ɗaya. Ya ce kwamitin zai ƙunshi wakilai biyar daga kowanne ɓangare, kuma za a ba shi makonni biyu domin ya miƙa rahotonsa. Ajaero ya jaddada cewa dole ne a yi la’akari da ra’ayin ƙungiyar NLC, kasancewar ita ce ƙungiya mafi girma a Afirka, don samun adalci da fahimtar juna.
A cewarsa, sakamakon aikin kwamitin ne zai tantance matakin gaba da za a ɗauka dangane da zanga-zanga, yajin aiki, ko kuma ƙauracewa amfani da hanyoyin sadarwa. Hakan na nufin matakin miƙawa gwamnati takardun ƙorafi da aka shirya yi zai tsaya har sai an kammala aikin kwamitin.
