“Tun ban fi shekara 18 ba na fara aikin gwagwarmaya”
Daga AISHA ASAS
A yanzu dai kai ya waye, kusan na ce birni da ƙauye mun aminta mace mai sana’a ita ce mace, wadda ba ta yi kuwa ta rako su ne. Muhimmancin sana’a ga ‘ya mace ba zai misaltu ba, hakan ya sanya a kullum ake faɗa tare da janyo hankalin mata kan neman na kai. A wannan satin filin mata a yau ya yi wa masu karatu babban kamu, inda mu ka ɗauko maku ɗaya daga cikin matan da su ka cancanci a kirasu da Gimbiya saboda jajircewa wuin neman na kai, tare da taimakon mata don ganin ba su dawamma a ƙunci ba, haka zalika ta kasance mai kishin mata ‘yan uwanta inda ta fito da tsari wanda zai taimake su su dogara da kansu. Aisha Asas tare da Hauwa Farouk Ibrahim:
MANHAJA: Masu karatu za su jin tarihinki a taƙaice.
HAUWA FAROUK: Masu bibiyan dandalin sada zumunta, sunana ba ɓoyayye ba ne, wato Hauw Farouk Ibrahim, wadda aka fi sani da (Women_Adɓocate). An haife ni a garin Kano ƙaramar hukumar Kumbotso. Na yi makarantar primary a ‘Best Way Nursery and primary school’, sannan na ci gaba da karatun makarantar gaba da ‘primary’ a ‘Collage of Art Science and Remedial Studies’. Na samu takardar shaidar diploma a ɓangaren na’ura mai ƙwaƙwalwa, a Audu Baƙo college of Agriculture Bambatta. Yanzu haka na samu takardar ƙarin karatu na digiri a Babbar Jamiar tarayya ta Dutse.
Wacce sana’a ki ke yi ko kuma me ki ka sa gaba yanzu?
Kusan in ce na fara harkar gwagwarmaya da aiki da ƙungiyoyi tun ban fi shekaru 18 ba a duniya, nayi aiki da ƙungiyoyi da dama na ƙasa da kuma Afrika bakiɗaya. Misali na yi aiki da ƙungiyar ‘International Foundation for Electoral System’ IFES, a matsayin ‘Election Monitor’, ‘National Democratic Institution’ NDI, da kuma ‘West African Network for peace building wanep’, inda a yanzu haka ina aiki da ƙungiyar ‘Dispute Resolution and deɓelopment initiatiɓe’ wadda aka fi sani da ‘Democratic Action Group’ (DAG) kuma ina da ƙungiyata ta kaina mai suna ‘Women Empowerment and Sustainable Deɓelopment Initiatiɓe’ (WESDI).
Yanzu haka dai ina sana’ar abinci, ina da ‘restaurant’ anan medile Jidda ‘chops and more, kuma ina ɗan taɓa kasuwanci, to yanzu babban abinda na sa a gaba shi ne harkar ƙungiyoyi da kuma wayar wa da mata kai, inda na ƙirƙiri wani ‘program’ mai suna ‘Matan Arewa’ wanda zai maida hankali akan kawo matsaloli da ƙalubalen da mata suke fuskanta da kuma ‘possible solutions’ wanda nan bada jimawa ba zan fara gabatar da shi a ƙarƙashin ƙungiyata mu dinga yaɗawa a shafukan sada zumunta. Da kuma haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu wajen taimaka wa mata a matakai daban daban.
Shin kafafen sada zumunta ci gaba ya kawo wa mata ko ci baya?
Ni a ganina gaskiya shafin sada zumunta ya kawowa mata cigaba sosai, musamman ta fuskar kasuwanci mafi yawa daga matan da suke amfani da shafukan sada zumunta a yanzu su na amfani da su wajen yin kasuwancinsu daga gida domin dogoro da kai, sannan akwai mata da yawa waɗanda suke da mabiya da yawa a shafukan sada zumunta, su na samun tallace tallace daga mutane ɗai ɗai, kuma su kan samu har a wurin kamfanoni wanda suke dogaro da kansu domin itama wannan ɗin kamar sana’a ce mai zaman kanta, babban abinda ya kawo wa mata ci baya a ‘social media’ ni dai a ganina bai wuce wata kafar sada zumunta ta ‘tiktok’ ba wadda zaki ga mata da yawa wai yanzu abin takaici, abin har yakai mata dattawa su na amfani da wannan kafar su na rawa ana yaɗawa duniya. Wannan babban abin takaici ne wanda ya kamata ayi saurin ɗaukar mataki akan hakan.
A matsayin ki ta mace ‘yar gwagwarmaya ko kin fuskanci ƙalubale?
Tabbas duk wasu al’amura na rayuwa su na ƙunshe da ƙalubale kala kala, wani lokacin nakanci karo da kalaman ɓatanci, ko wasu kalamai da zasu taɓa mutuncina da martabata, yana da wahala na maida raddi ga masu irin wannan ɓatancin, na kan hango abubuwan da nake so na cimma a gaba a rayuwata, sai na faɗa wa kaina cewa dukkan wani abu da zaka yi a rayuwa to tabbas za ka gamu da ƙalubale kala kala kuma dole nasara tana tattare da waɗannan abubuwan shiyasa ba su cika damuna ba.
Kin zaɓi sana’ar abinci. Ko me ya sa ki karkata kan wannan sana’ar?
Kowanne mutum akwai abinda yakeso kuma yake kwanta masa a rai, nakan kasance a cikin nishadi a duk lokacin da nake girki, hakan ce tasa na fara tunanin me zai hana na fara sana’ar abinci koda a gida ne, saboda a lokacin ina aiki, to kuma ina tunanin dama wacce sana’a zan fara bayan aikin da nake wanda zai taimaki rayuwata , bayan dogon nazarin da na yi akan rashin gidan abinci a yankin da nake da kuma buƙatar abincin a wannan yankin, sai na ga buƙatar buɗe gidan abinci don sauƙaƙa wa al’ummar da ke hada hada a wannan yankin. Kuma Alhamdu lillah mun fara cikin nassara kuma ana kai har yanzu. Domin har takai ana karɓar kwantiragin masu biki, suna da tarurruka daban daban.
Wane irin ƙalubale ki ka fuskanta a ɓangaren sana’arki ta abinci?
ƙalubalen da nake fuskanta gaskiya a wanna sana’a na farko kinga dole akwai jajircewa a ciki domin sana’a ce da za a fito tun safe a koma da dare mafi yawancin lokuta zaki fa baka da wani lokaci na kanka. Sannan abu na biyu sakamakon haɗa aikin abincin da na ke yi da kuma aiki da na ke yi na kan shafe wasu kwanaki ko awanni banje shagon abincin ba, akwai masu kula da komai. ƙalubalen bai wuce rashin samun ishashen lokacin zama a wajen ba, domin na zanga wasu abubuwa da suke ba daidai ba idan na dawo daga aiki da dole sai ka tsawatar wanda idan ba ka wajen bai zama dole ayi ɗin ba. Sannan kuma duk wani abu da za a ce wani zaka sa a kai to dole sai ka yi haƙuri amma alhamdu lillah ba laifi suna matuƙar ƙoƙari da kuma jajircewa.
Menene muhimmancin girki ga ‘ya mace?
Girki yana da matuƙar mahimmanci a wajen ‘ya mace, duk kyawunki, duk iya kwalliyarki idan ba ki iya girki ba, ba ki cika mace ba, ke da kanki idan kin iya girki za ki ji kamar ke wata ta musamman ce a cikin mata, sannan kuma iya girki yana kawo shaƙuwa tsakanin ki da mijinki. Zai kasance duk inda yaje yaci abinci idan ba ya dawo yaci nakin ba bazai taɓa jin daɗi ba.
Iya girki zai taimaka miki wajen gane wanne abinci ne mai ƙara lafiya da gina jiki da za ki dinga dafawa iyalinki. Wane abinci ya kamata ki dafa a kuma dai dai wane lokaci. Zai taimaka miki wajen dafa/sarrafa abinci kala kala, kusan ko da yaushe akwai kalar abincin da za ki dafa, wani abin za ki yi sati baki maimaita shi ba, domin gamsuwar iyalinki. Iya girki kuma zai taimaka wa iyalinki wajen rage kashe kuɗi, misali irin’ snacks’ ɗin nan idan wata hidima ta taso zanki yi komai da kanki babsai kinbje kin siya a waje ba wanda hakan zai taimaka sosai wajen rage kashe kuɗi.
Wannan ƙungiyar taki ta taimaka wa mata ne ta ɓangaren abin amfanin yau da kullum, ko ta ɓangaren matsalolin da suka addabe rayuwarsu?
ƙungiyar ‘Women Empowerment and Sustainable Deɓelopment Initiatiɓe’ (WESDI) tana taimaka wa mata ta ɓangare daban daban na amfanin yau da kullum da kuma ɓangaren gyara ga matsalolin da mata suke fuskanta, da wayar da kan mata domin su dogara da kansu, ƙarfafa musu gwiwa su nemi ilimi, koyawa mata ƙananun sana’oi domin dogaro dakai, da dai sauransu. Muna kai kuma insha Allah zabmu cingaba da neman taimako ko haɗin gwiwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu dan ganin an tallafa wa mata a matakai daban daban na rayuwa.
Mu koma ɓangaren Iyali, ko akwai?
Bani da aure gaskiya, kuma ban taɓa yin aure ba. Amma kwanan nan in sha Allahu zan shiga daga ciki.
To Allah ya kawo mafi alkhairi.
Amin.
Wane irin kaya ki ka fi sawa?
Gaskiya nabfi saka dogayen riguna. Kaso 90 a cikin 100 na kayan sawa na dogayen riguna ne.
Wane abinci ya fi kwanta miki a rai?
Uhm gaskia a abincin da ya fi kwanta min a rai nabfi son shinkafa da haɗin salad kowanne irin sarrafawa za a yi mata, sannan ina son dambu da kuma ɗan wake.
Shin kwalliya za a iya kiran ta da dole ga ‘ya mace?
Kwalliya da tsaftar jiki ya zama dole ga ‘ya mace, kwalliya da yin ado ga ‘ya mace na da matuƙar muhimmanci. Shi ya sa Hausawa kan yi wani karin magana da “mata adon gari.”
Kwalliya na da muhimmanci ga ‘ya mace domin ta kasance tamkar ita ce jarinta. Kwalliya na ƙara wa mace ƙima da daraja a idon jama’a. Duk duniya duk inda aka ce ga wata mace to za a yi tsammanin ganin ta caɓa ado da kuma yin kwalliya, sannan ke a karan kanki idan ki ka yi kwalliya za ki ji daɗin jikinki ba sai lalle dan za ki fita ba, ya zama dole mata mu kula da tsaftar jikinmu da kuma yin kwalliya.
Me ke saurin ɓata ma ki rai?
To babban abinda ke ɓata min rai shi ne raini, haƙiƙa ina matuƙar ƙoƙarin ganin cewa na girmama kowa wanda yake ƙasa da ni da kuma waɗanda suke sama da ni, shi yasa ko irin wasan banza na ka gaya wa mutum baƙar magana ko ka zages hi ya rama gaskiya ban iya ba. Mutuncina ya fi min komai a rayuwa. Sannan ƙarya, munafurci da kuma ‘pretending’ yana daga cikin abinda yake saurin ɓata min rai gaskiya.
Shin akwai wani abu da ki ka taɓa cin karo da shi da ya ɓata maki rai, wanda ki ke ganin don ki na mace ne aka yi maki shi?
Tabbas kam naci karo da abubuwa da dama wanda nake ganin cewa don ina mace ce aka yi min, wasu lokutan ma har nakan magantu na ce me ya sa ake yi wa mata haka ne?
Na kan yi magana akan mazajen da suke haifar ‘ya’ya barkatai kuma ba sa iya kula da su, ina matuƙar ƙoƙari wajen fahimtar da mutane amfanin haihuwa da kuma haƙƙin da yake kan duk wanda ya haifa ɗin, saboda a ganina matsalolin da muke fuskanta a Arewacin Nijeriya na rashin tsaro yana da nasaba da haihuwar ‘ya’yan da ba za a iya kula da su ba. So nakan samu wasu daga cikin mutane masu ƙarancin fahimta da zasu dinga ganin cewa ni mace ce mema na sani akan harkar iyali da zanzo ina irin waɗannan maganganu da sauransu.
Sannan kuma a lokacin da aka bani ‘Acting President’ ta ƙungiyar ɗalibai ta Audu Baƙo College of Agriculture Dambatta SUG, na fuskanci ƙalubale kala kala har da masu rubutu akan hakan cewa bai kamata a bar makaranta a hannun mace ba da dai sauran ƙananun maganganu wanda hakan ba su haifar min da komai ba sai alkhairi, domin a ƙarshe sai da aka bani lambar yabo na mace ta farko da ta fara shugabantar ɗalibai a wannan makaranta. Kuma alhamdu lillah har yanzu ɗaliban da muka bari suna tunawa da mu idan abu ya faru za a ambace ka a maka fatan alkairi. A ranar da na je kai musu ziyara suna matuƙar murna da kuma kewa.
Wacce shawara za ki ba wa mata ‘yan uwanki?
Shawarar da zan ba wa mata shi ne su dage su nemi ilimi, saboda ilimin ‘ya mace yana da matuƙar amfani wajen samun nagartacciyar alu’mma, kada ki ce wai kin tsufa ba za ki nemi ilimi ba, a’a shi ilimi ba ya tsufa, sannan abu na biyu mata mu dage mu nemi sana’a komai ƙanƙantar ta, wadda za ki dogara da kanki, domin mai baka yau da gobe zai ga cewa kamar ka zama wani nauyi akansa, idan kuwa kina sana’a ko yaya ne za ki taimaka wa kanki da kuma ‘family’ ɗinki, sannan abu na ƙarshe mu cire ƙyashi da son zuciya da kuma hassada, yau idan akace mace takai wani mataki lallai mu dafa mata mu taimaka mata ba wai mu dinga ƙalubalantar ta ko kuma yaɗa ƙarya ko zaginta. Allah ya sa mu dace amin.
Amin. Mun gode da lokacinki.
Ni ma na gode kwarai.