Ƙungiyar Manoma ta bayyana damuwarta kan yaɗuwar taki mara inganci a jihar Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN), reshen Jihar Jigawa ta nuna damuwarta kan yadda ake samun yawaitar gurɓataccen takin zamani a kasuwanni, tare da samun yawaitar hauhawar farashin takin tare da faɗuwar farashin kayan anfanin gona.

Shugaban ƙungiyar reshan jihar, Injiniya Auwalu Garba Ibrahim ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan da gudanar da taron ƙungiyar na jihar a Birnin Dutse yayn da yake zantawa da manema labarai.

Ya buna takaicinsa kan yadda taki marar kyau yake neman cika kasuwanni a faɗin jihar, wadda hakan na iya zama wata barazana ga manoma, don haka ƙungiyar manoman ba zata bari wasu miyagu marasa kishin jihar su riƙa shigo da gurɓataccen takin ba suna ƙoƙarin cutar da manoma.

Ya ƙara da cewa, ƙungiyar za ta ɗauki dukkan matakin da zata hana yaɗuwar gurɓataccen taki a dukkanin kasuwannin jahar, da nufin hana cutar da manoman jihar Jigawa.

Ya ci gaba da cewa, za su haɗa gwiwa da masana harkokin takin waɗanda suke da ilimi kan takin zamani wajan kama dukkan takin da ba shi da kyau da nufin yin waje da shi daga faɗin kasuwannin jihar.

A ɗaya ɓangaren kuma, ƙungiyar ta nuna gamsuwarta da jin daɗi kan hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke akan tabbatar da Faruƙ Mudi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar na ƙasa bayan doguwar shari’a da aka yi da shi tsawon shekaru.

Malam Auwalu Garba ya gode wa Kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasa da ta zartar da hukunci bisa adalci da kuma cancanta, ya ce, hakan ya nuna kwarewa da samun aiki tare da adalci a wajen alƙalan kotun da suka tabbatar da hukuncin, domin kotun ta yi hukuncin da ya dace ba tare da nuna son zuciya ba.

Ya ci gaba da cewa, sakamakon rashin shugabanci a baya ya sa manoma da dama sun yi aasara mai yawa lokacin da ƙungiyar ta faɗa matsalar rashin shugabanci domin abin da ya kamata su samu basu samu sakamakon rikicin da ƙungiyar take yi na rashin shugabanci a matakin tarayya da kuma wasu jihohi.

By ukarofi