Ƙungiyar NASU a Jami’ar Nasarawa ta gudanar da babban taron ta na ƙarshen shekara

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Babbar Jami’ar Gwamnatin Jihar Nasarawa waɗanda ba na ilimi ba da ake kira NASU a turance sun gudanar da wani babban taronsu na ƙarshen shekarar 2024.

Da yake jawabi a wajen taron shugaban kungiyar a jami’ar kwamarate Danjuma Mohammed Namalama ya ce sun ga yadace ne su gudanar da taron don samun damar tattauna da kuma murnar ganin karshen shekarar ta 2024 tareda karrama wasu shugabanni da mahimman mutane da suke bai wa ƙungiyar cikakken goyon baya akoyaushe musamman shugabar babbar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da kokari da take yi wajen daukaka harkokin ilimi da sauran bangarori a jami’ar kawo yanzu.

Kwamared ɗanjuma Mohammed Namalama ya kuma bayyana wasu nasarori da dama da ƙungiyar ta NASU a jami’ar ta cimma a karkashin jagorancin sa da suka hada da sayin wata motan haya don samo wa ƙungiyar kudin shiga da ginin babbar sakatariyar ƙungiyar a jami’ar da bin hakin ‘ya’yan ƙungiyar da tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin ƙungiyar da mahukuntan jami’ar da sauran su inda yace duka nasarorin ya iya cimma ne sakamakon cikakken goyon baya da yake samu daga mambobin sa na ƙuniyar inda ya bukace su su cigaba da ba shi cikakken goyon bayan kana yayi musu fatar alheri ayayin da suka munar karshen shekarar ta 2024.

Daga nan sai shugaban ƙungiyar ta NASU kwamarete Danjuma Mohammed Namalama ya kuma yi amfani da damar inda ya bukaci mahukuntan jami’ar su cika duka alkawura da suka yi wa ƙungiyar na biya musu sauran basussuka da hakokin su da sauran su.

Ita ma da take jawabi shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta gingina wa hangan nesa na kira babban taron karshen shekarar da ƙungiyar tayi karkashin jagorancin Danjuma Namalama inda tace tabbas hakan yadace don sai bai da damar gana da juna tsakanin mambobin.

Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kuma yi alkawarin duba bukatun da ƙungiyar ta gabatar tareda biya musu duka hakokin su da suke bin jami’ar a hankali kana ta gode wa ƙungiyar dangane da bata lambar yabo ta musamman da suka yi.

Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi a wajen bikin duk sun yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar na haɗa kan mambobin ta waje guda sa’anan an bai wa wasu daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron lambobin yabo na musamman ciki har da ita Farfesa Sa’adatu Hassan Liman.

By ukarofi