Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Arewa sun gudanar da babban taro a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A ’yan kwanan nan ne wata hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Kasuwar Arewacin Kasar nan bakidaya da ake kira ‘Northern Traders Association’ a Turance wadda ta kunshi duka jihohin arewa na kasar nan 19 ta gudanar da wani gagarumin taron ta a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa don tattauna wasu matsaloli da kalubale da ke addabar ’ya’yan kungiyar bakidaya.

A jawabin sa na maraba Shugaban kungiyar na kasa alhaji Baba Usman Jos wanda mataimakin sa alhaji Jahi Abdullahi ya wakilce shi ya bayyana cewa kungiyar ta ga ya dace ne ta hada babban taron don samun damar tattauna akan wasu matsaloli da ’ya’yan qungiyar ke fuskanta musamman wadanda ke tafiye-tafiye akan manyan hanyoyin kasar nan don harkar su ta kasuwanci don kare hakokin su ta hannun ’yan custom da ‘yan sanda da wasu ‘yan bangan hanya da ke tsare hanyar suna cin tarar mambobin su ba gaira ba dalili.

Hakan ya sa Alhaji Baba Usman Jos yayi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga duka gwamnatoti a duka matakai su rika sa ido tare da takawa wadannan ire-iren hukumom kungiyar da sauran su birki.

Ya ce ba shakka ayyukan kungiyar ta ’yan kasuwar arewacin kasar nan ta dade tana tallafa wa kokarin gwamnatoci don rage zaman banza da inganta harkokin kasuwanci don bunkasar tattalin arzikin kasar nan baki daya da sauran su, inda ya ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda wadannan hukumomi ke cigaba da take hakkokin mambobin nasu a kowanne lokacin.

Daga nan sai Shugaba Alhaji Baba Usman Jos ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana wasu hanyoyin tara kudaden shiga wa kungiyar kana ya bukaci duka mambobin kungiyar su cigaba da hada kai su kuma riqa bin dokokin kungiyar.

Shima anasa bangaren da yake jawabi kodinetan kungiyar na reshin jihar Nasarawa wanda shi ne mai masaukin baqi wato da ya samu wakilcin alhaji Sabo Barau ya gode wa kungiyar dangane da zabin jihar ta Nasarawa a matsayin wajen gudanar da taron a karon nan inda ya ce ba shakka taron bayan gano hanyoyin warware matsaloli da qungiyar ke fuskanta a yanzu zai kuma je nesa ba kusa ba wajen hada kawunan duka mambobin ta a arewacin kasar nan baki daya.

Ya kara da cewa, duk da bai samu damar halartar taron ba a shirye yake ya cigaba da bada nasa gagarumin gudumawa wajen cigaban kungiyar a kowanne lokacin.

Shi kuma maimartaba sarkin Lafiya Alhaji Sidi Bage mairitaya bayan ya jinjina wa hangan nesa da ’yan kungiyar suka yi na kira taron ya kuma gode musu dangane da zabin garin Lafiya fadar gwamnatin jihar ta Nasarawa a matsayin wajen taron inda ya tabbatar musu cewa masarautar sa zata cigaba da basu cikakken goyon baya don ba su damar gudanar da harkokin su na kasuwanci yadda yakamata.

Sauran manyan baki da suka halarci babban taron mai dimbin tarihi sun hada da wakilin kwamishinan ’yan sandan jihar Nasarawa da ’yan siyasa da manyan ’yan kasuwa daga ciki da wajen arewacin kasar nan bakidaya inda duk a jawabin su sun yi fatar alheri wa kungiyar.