An dakatar da kocin Union Berlin kan naushin ɗan wasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An dakatar da kocin kulob ɗin Union Berlin Nenad Bjelica wasanni uku saboda naushin dan wasan Bayern Munich Leroy Sane a fuska.

Lamarin ya faru ne a minti 74 na wasan da suka buga a Bundesliga a ranar Laraba, lokacin da Sane ke kokarin daukar kwallo a hannun Bjelica yayin da ta fita jifa.

Bjelica wanda aka ci tarar yuro 25,000 sau biyu yana sa hannu a fuskar Sane, yana tura shi, amma daga baya an kore shi daga wasan.

Ya nuna dabi’ar da ba ta ’yan wasa ba, kamar yadda hukumar kwallon qafa ta Jamus ta bayyana.

Dan kasar Croatian mai shekara 52 shi ke jagorantar kungiyar tun watan Nuwamba, yanzu kuma ba zai halarci wasan da za su yi da Darmstadt da RB Leipzig da kuma Mainz.

Union da suka kammala gasar a matsayi na hudu a bara, sune matsayi na 15, da tazarar maki uku tsakaninta da ukun karshe.

Bayern na matsayi na biyu, da maki hudu tsakaninta da Bayer Leverkusen, bayan nasarar da ta yi da ci 1-0.