Ganduje ya kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Sheikh Yusuf Ali

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Sheikh Iman Dr Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya) jiya Alhamis.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya nuna alhininsa bisa rasuwar shehin malamin sannan ya jaddada cewa rashin Shehun ba wai na iya iyalansa ba ne shi kadai, rashi ne nasu su aminansa da kuma al’ummar duniya.

“Saboda Sheikh Yusuf Ali ya karar da rayuwarsa ne gabadaya kan yada addinin Musulunci da jan hankali kan koyarwarsa,” inji Ganduje.

Tawagar ta Shugaban Jam’iyyar ta hada da dukkan wani mai fada a ji a cikin jam’iyyar APC tun daga kan Shugaban Jam’iyyar na jiha Alhaji Abdullahi Abbas da Hon. Murtala Sulen Garo da Sanata Kabiru Gaya da Hon. Mutari Ishaq da Sheikh Haroon Ibn Sina da SA Hon Abubakar Aminu Ibrahim da Chairman Hon. Habu PA da Hon. Nasiru Usman Zico, Abba Ganduje da sauran jiga-jigan jam’iyya da masoya da magoya baya.