Ɗauke ragamar sassan CBN zuwa Legas: Cika baki kawai kuke, cewar Sanusi ga ’yan siyasar Arewa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi, ya ce “surutu” kawai ‘yan siyasar Arewa ke yi dangane da shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na dauke ragamar gudanarwa na wasu sassan bankin daga Abuja zuwa Jihar Legas.

Sanusi ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa da su yi watsi da surutan da ‘yan siyasar Arewa ke yi kan batun saboda a cewarsa, Abuja a matsayin Babban Birnin Tarayya ba matsalar Arewa ba ne.

Idan dai za a iya tunawa, tun bayan da CBN ya bada sanarwar shirinsa na dauke wasu muhimman sassan CBN daga Abuja zuwa Legas, aka yi ta ce-ce-ku-ce a sassan kasa.

Lamarin da wasu ‘yan siyasa musamman daga Arewacin Nijeriya, suke ganin hakan ba zai sabu ba,  tare da gargadin irin sakamakon da daukar wannan mataki zai haifar.

Jaridar Intelregion ta raiwato cewa, a wata sanarwa da ya fitar, Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi, ya nuna goyon bayansa kan kudurin CBN din, yana mai cewa hakan ya yi ma’ana.

Sanusi ya yi kira ga Gwamnan CBN Yemi Cardoso, da ya yi la’akari da mata masu ‘ya’ya da masu matsalar rashin lafiya yayin da ya tashi dauke bangarorin CBN zuwa Legas.

By Editor