Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Sakkwato

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Aliyu Ahmad din ne a zaman da ta yi ranar Alhamis inda ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben da Aliyu ya samu a zaben 2023.

A hukuncin kotun, wanda Mai shari’a Tijani Abubakar ya karanta, ya yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Ahmed Aliyu.

Kwamitin alkalin ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke na cewa PDP ta kasa tabbatar da zargin magudi da rashin bin dokar zabe ta 2022.