Kotun Ƙoli ta ayyana Fubara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Ribas

Daga BASHIR ISAH

Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta ayyana Sim Fubara a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a Jihar Ribas.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis bayan da ta karbi bayana daga bangarorin da shari’ar ta shafa.

an takarar gwamnan na Jama’iyyar APC a jihar a zaben 2023 da ya gudana, shi ne ya daukaka kara inda ya kalubalanci nasarar da Gwamna Fubara ya samu a zaben.

Nasarar Fubara  a Kotun Kolin na zuwa ne a daidai lokacin da ruwa ke ci gaba da tsami a tsakaninsa da Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.