Tasirin marubuci a cikin al’umma tamkar tasirin gishiri ne a cikin miya – Hauwa Shehu

“Yawaitar matsalolin damfara da satar bayanai a yanar gizo ya sa na rubuta ‘Harin Gajimare”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Rubutun adabi abu ne da ke buqatar samun jigo mai karfi da zai ja hankalin masu karatu, kuma su amfana da darussan da marubuci ya sarkafa cikin labarinsa, bayan bincike mai zurfi da nazari mai kyau. Wannan shi ne irin tunanin da marubuciya Hauwa Shehu ke son sauran marubuta su fahimta, a kokarinta na fadakar da su yadda za su inganta rubutunsu na onlayin da yake kara samun karbuwa a tsakanin marubuta. Wannan jarumar marubuciya da ta kasance gwarzuwa ta farko a gasar cibiyar ilimi ta Gusau Institute ta shekarar 2023, ta nuna bajinta ne da littafin ta na farko ‘Harin Gajimare’ wanda ya zo da wani sabon salo da ba kasafai marubuta ke mayar da hankali a kansa ba. Bayan zamanta marubuciya, har wa yau tana da masaniya a bangaren ilimin tsaron giza-gizan sadarwa da fasahar zamani. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Hauwa Shehu ta bayyana burinta na samar da wata cibiya da za ta rika horar da marubuta ilimin fasahar zamani da cigaban rayuwa.

MANHAJA: Mu fara da sanin wacce ce bakuwar mu ta wannan mako?

HAUWA SHEHU: Cikekken sunana shi ne Hauwa Shehu. Ni malamar makaranta ce kuma marubuciya, mai aikin wayar da kan al’umma kan abin da ya shafi tsaron yanar gizo. Har wa yau kuma ni ‘yar kasuwa ce mai fassara finafinan ketare zuwa harshen Hausa, ina kuma shirya tallace-tallace, na ‘yan siyasa, kamfanoni da ‘yan kasuwa wato jingles, karkashin kamfanina na KFF Multimedia. Sannan ina tava ayyukan kungiyoyi masu zaman kan su (NGO).

Menene cikakken tarihin marubuciyar?

Ni ‘yar asalin Jihar Kano ce, daga Karamar Hukumar Nasarawa. Na yi makarantar firamare ta Gwagwarwa Primary School, da karamar sakandire (J.S.S) ta Maikwatashi a Kano. Sannan na yi babbar sakandire a GGSS Maimuna Gwarzo a Kaduna. Na halarci Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Kano, wato CAS, inda na samu shaidar Diploma a fannin ilimin Lissafi. Na kuma yi Digirina na farko a kan fannin koyar da Ilimin Lissafi a makarantar Horar da kwararrun Malamai da ke Kaduna, ta National Teacher’s Institute Kaduna.

Na kuma yi karatu a bangaren ilimin addini, inda a nan ma Allah Ya nufa na samu damar sauke Alkur’ani mai girma. Na yi aure, kuma Allah Ya albarkace ni da ‘ya’ya mata guda uku. Ina zaune a garin Kano da iyalina.

Yaushe ki ka fara rubutu, kuma menene silar fara rubutunki?

Na fara dasa alqalamina a littafi da sunan saqa kirkirarren labari ne a qarshen shekarar 2009 zuwa farkon 2010. Silar fara rubutuna kuwa ya samo asali ne tun lokacin ina aji shida a makarantar firamare, sakamakon wani abu da ya faru na tsoratarwa da ‘yan ajinmu suka yi mini, da na je kai kara tsabar haushin abin da aka yi mini ne ya sa na kasa magana sai hawaye, ganin haka ya sa malaminmu ya ba ni takarda ya ce na je na rubuto masa abin da ya faru. Na rubuta kuma na kai masa, ya karanta a gaban aji sannan ya yi musu hukunci. Yadda na ga na isar da sakon zuciyata a rubuce kuma kwalliya ta biya kudin sabulu sai hakan ya hura min wutar son zama marubuciya. Tun daga nan kuma kofar rubutu ta bude. Alhamdulillah.

Yaya farkon rubutunki na adabi ya kasance, kuma wa ya tallafa miki ki ka fitar da littafinki na farko?

Littafin ‘Harin Gajimare’ shi ne cikakken littafina na farko, wanda kuma da shi ne na samu nasara a Gasar Gusau a shekara 2023. Sannan ubangidana da ke taimaka min da shawarwari kan rubutu, Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano shi ya tallafa min da shawarwari da gyare-gyare, har dai na samu na kammala shi.

Ko za ki gaya mana sauran littattafan da ki ka rubuta da takaitaccen bayani kan wasu daga ciki?

Dogayen labaran da na rubuta guda uku ne. ‘Shukuriyya’, ‘Zumuncin Jini’ da kuma ‘Harin Gajimare’. Sai kuma gajerun labarai masu yawa da na rubuta.

Shi ‘Harin Gajimare’, wanda shi ne littafina na farko, labari ne a kan iftila’in kutsen na’ura, samfarin garkuwa da kundin bayanai na kwamfiyuta, wato a turance Ransomware Attack, da ya afkawa wani masha’urin kamfani, a lokacin da suke tsananin bukatar kundin.

Shi kuma littafin ‘Shukuriyya’ yana dauke ne da wani labari da ya yi duba a kan kalubalen da yara ‘yammata masu tasowa, da ke shekarun balaga, ke fuskanta a makarantun sakandire musamman idan suka kasance masu kwazo. Ya taba matsalar kabilanci da kuma sakacin iyaye wajen barin ‘ya’yansu suna yawan fita da sunan daukar darasi na musamman (Lesson) a wani waje.

Sannan sai littafin’ Zumuncin Jini’, wanda labari ne da ya yi magana a kan yadda wasu iyaye ke nuna fifiko a tsakanin ƴaƴansu ta hanyar kambaba kokarin wani dan wani kuma a kushe nasa kokarin da nuna gazawarsa, ba tare da la’akari da kowanne dan’adam yana da irin tasa dabi’ar da kuma baiwar da Allah Ya yi masa. Dalilin hakan ne yake jawo a samu takun saka tsakanin yara ‘yan’uwa na jini da daya, saboda wutar gabar da iyaye suka kunna.

Littafinki na ‘Harin Gajimare’ ya zo da wani sabon salo da ba a saba da shi ba, ko za ki gaya mana menene ya ja hankalinki ga daukar wannan jigo?

Abin da ya ja hankalina wajen daukar jigon shi ne yawaitar matsalolin damfara da satar bayanan da ake yi ta yanar gizo, wanda hakan babbar barazana ce ga duk wani mai amfani da na’ura, walau kwamfuta ko wayar hannu. Wannan dalilin ne ya sa na ga dacewar ba da tawa gudummawar wajen wayar da kan al’umma su fahimci girman matsalar da hanyoyin kauce mata, ta hanyar saka labarin ‘Harin Gajimare.’

Kin taba shiga wata gasar rubutu, kuma ko kin yi nasara?

I, na shiga gasanni daban-daban, wasu na yi nasara wasu kuma Allah bai nufa ina daga cikin masu nasara ba. Na tava shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2021 kuma labarina har ya kai matakin da alkalai suka ce ya cancanci yabo cikin 12 na farko, har ma sun aiko mini da shaidar shiga gasar. Na kuma taba shiga gasar Gusau sau biyu, kuma na yi nasara a 2023 a mataki na farko, har na karbi kambu. Sannan na taba shiga gasar Zauren Marubuta na manhajar WhatsApp, amma ban yi nasara ba.

Yaya ki ka ji da nasarar da littafinki na ‘Harin Gajimare’ ya samu a Gasar Gusau Institute?

Alhamdulillahi, wannan nasarar da ta zo a lokacin da ban tsammace ta ba, ta ninninka kalubalen da na fuskanta a baya. Babbar nasara ce a ambace ka a inda ka ke ganin karanka bai kai tsaiko ba. Nasara ce ta cuxanya da mutane na kwarai masu daraja, wanda rubutu ne silar hakan. Nasara ce da sunanka ya kai inda kai ba ka isa ka je ba, ba don ka shiga rigar alfarmar rubutun ba. Ga tagomashin samun kyaututtuka, Alhamdulillah.

Yaya ki ke gani marubuta za su rika zakulo irin wadannan jigogin don kawo gyara ga wasu matsaloli da suke jan hankalin duniya?

Marubuta ‘yan baiwa ne, don haka hanyar ba mai wahala ba ce a gare su, kawai abin da zan iya cewa shi ne; su kasance da idanuwansu da  kunnuwansu a bude a kan al’amuran yau da kullum da ma halin da duniya ke ciki, ta haka ne za su zakulo ire-iren matsalolin da ke addabar duniya. Sannan abu mafi mahimmanci su yawaita bincike.

Wadanne hanyoyi ki ke bi wajen zabar jigo idan za ki yi rubutu?

Daga cikin hanyoyin da nake bi wajen zabar jigon rubutun da zan yi akwai kallon matsalolin da ba a fiye mayar da hankali a kansu ba. Sannan ina iya samun jigo ta hanyar wani abu da na gani a zahiri, a fim ko ma a rubutun da bai dara jimla daya ba.

Ya ki ke kallon rubutu a jiya da yau ta fuskar cigaba da koma-baya?

Idan muka kalli yanayin rubutu a yau to, kai tsaye zan iya cewa an samu cigaba ta fuskar saukaka hanyar rubutun, yaduwarsa da kuma wayar da kan kananan marubuta, wanda hakan babbar dama ce ga kowanne marubuci mai tasowa.

Sai dai duk da haka ana samun koma-baya ta fuskar kimar rubutun yau da kallon da ake yi wa marubutan yau din, wanda ya sha bambam da na jiya. Watakila hakan na da nasaba da yadda wasu daga cikin mu suke amfani da alkalaminsu wajen yada sakon da ya sava da tarbiyyar Malam Bahaushen da ake wakilta.

Me za ki iya cewa game da tasirin marubuta a cikin al’umma?

Marubuta ‘yan baiwa ne, wadanda suke amfani da baiwar da Allah Ya ba su wajen zakulo matsalolin da ke addabar al’umma su kuma warware ta  cikin hikima da basira. Tasirinsu a cikin al’umma tamkar tasirin gishiri ne a cikin miya, mahimmancinsu tamkar mahimmancin ruwa ne ga rayuwa. Domin sai an rubuta za a karanta, sannan sai an karanta za a fahimta, kuma sai an fahimta za a sani. Kazalika sai an sani za a amfana har a ribaci rayuwar duniya da ma ta lahira.

Duk wani abu na rayuwa tattare yake da kalubale da nasarori, ko za mu iya sanin wasu daga cikin nasarori da kalubale da suka shafi rayuwarki ta rubutu?

Kalubalen da na samu bai wuce fadi tashin neman hanyar da zan shigo jerin marubuta masu isar da sakonninsu ta hanyar rubutu ba, da yadda za a yi na fitar da littafi nima har a karanta. A lokacin da nake wannan gwagwarmayar duk wanda na ji an ce marubuci ne ko marubuciya ce to, take nake bibiyarsa musamman a manhajar Facebook. Wani lokaci har magana nake yi musu na tambaye su, ya za a yi na zama marubuciya kamar su?

Wasu su amsa min, wasu kuma su ki amsa ni. Amma duk da haka duk wani abu da ya shafi marubuta ban daina bibiyarsa ba, duk kuwa da na dan jingine alkalamin na wucin gadi a wancan lokacin.

Idan da za a ba ki damar kawo sauyi a wasu matsaloli da ke ci wa marubuta tuwo a kwarya da wacce matsala za ki fara?

Yawancin matsalolin da ke ci wa marubuta tuwo a qwarya, ina ganin an dauko hanyar kakkabe su, ko ma na ce wasu a yanzu an share babinsu, sakamakon kafa zauruka na musamman a manhajar WhatsApp, inda ake hada kan marubuta da samar mana da horo da fadakarwa kan ka’idojin rubutu, da hanyoyin da za mu inganta rubutunmu. Sai dai duk da haka ni akwai abin da nake kallo a matsayin matsala wani kuma zai iya kallon shi a matsayin nasara. Idan aka ce na fara da nawa kallon to, tabbas zan fara ne da kallon matsalar yawaitar kananan kungiyoyin marubutan Hausa, domin hakan barazana ce da za ta iya kawo rarrabuwar kan da ka iya jawo wa marubuta masu tasowa koma-baya.

A ganina idan aka dunkule ta hanyar samar wa kananan kungiyoyi wata uwa ko kuma na ce wata bishiyar da kowanne marubuci zai shiga inuwarta to, tabbas amon marubuta zai fi tashi ya ratsa ko’ina, su kuma ci gajiyar baiwarsu ta yadda za a ci gaba da  damawa da su a cikin gwamnati. Har su yi karfin da idan suka yi kira ba Gwamna ba, hatta sugaban kasa zai ji amonsu. Babu laifi idan bishiyar ta yi yado ta fitar da rassa zuwa sassa-sassa na fadin kasar nan, ko ma duniya bakidaya.

Misali a samar da gamayyar qungiyoyin marubuta da za su rika tattaunawa karkashin jagoranci da inuwa daya, kuma su rika magana da yawu daya.

Yaya alakarki take da marubuta da kuma masu karatun littattafanki?

Kasancewar marubuta mutane ne masu fikira da fahimta, alakarsu da kowa ma za ka same ta faran-faran. Sannan kuma ni shaida ce saboda kasancewata dxaya daga cikinsu?  Saboda haka ba ni da wata tsattsamar alaka da kowa sai zazzaka. Suna da girmamawa da mutunta juna a tsakaninsu. Alakata da masu karatu kuma sai son barka. Alhamdulillahi.

A cikin jerin marubutan onlayin da masu bugawa su wane ne gwanayenki? Wadanda ki ke kallo a matsayin allon kwaikwayo ko iyayen gida?

Ni fa duk wani marubuci gwanina ne, domin ina girmama baiwar da Allah Ya ba su. Amma idan ka ce na rarrabe to, maganar gaskiya ban karanta wasu littattafai da yawa na onlayin ba, sai dai abin da ba za a rasa ba, daga cikin wadanda salonsu yake birge ni akwai

Nana Aicha Hamissou Abdoulaye, Hassana Suleiman (Sanah), Hassana Danlarabawa, da Hadiza D. Auta. Sai kuma a tsofaffin marubuta masu talifi akwai Sadiya Garba Yakasai, Fauziyya D. Sulaiman, Bala Anas Babinlata, Danladi Haruna, da kuma Abdullahi Hassan Yarima.

Jibrin Adamu Jibrin Rano wato Abu Amrah, shi ne bijimin malamina kuma allon kwaikwayona, wanda nake gurfana a gabansa domin daukar darasin da ya shafi adabi. Babu kyashi ya ba ni gagarumar gudummawar da ta ba ni damar gyara  alkalamina har na shigo ake damawa da ni. Kuma hakika kowanne mataki na taka a duniyar rubutu ba zan manta da wanna gagarumar  gudummawar da ya ba ni ba. Sai kuma Malam Yusuf Yahaya Gumel, saboda shawarwarin da yake ba ni.

A wane yanayi ki ka fi jin dadin yin rubutu, kuma me ya sa?

Gaskiya ni idan rubutu ya zo mini a kowanne irin yanayi ina iya yi kuma ina jin dadin hakan, amma dai na fi son yi idan na kevance kaina saboda na fi samun nutsuwa. 

Wacce kungiyar marubuta ki ke ciki?

Ni mamba ce a Kungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano ta GAMJIK, kuma ina rubutu karkashin kungiyar Taurari Writers Association.

Wace shawara za ki bai wa sababbin marubuta da masu sha’awar fara rubutu?

Shawarar da zan bai wa sabbin marubuta masu sha’awar fara rubutu shi ne, da farko su fahimci irin baiwarsu, da sakon da suke son isarwa. Sannan su tsarkake niyya su tabbatar sun yi bincike a kan abin da suke so su yi rubutun a kansa, kada su yi gaggawa domin sannu-sannu ba ta hana zuwa. Su jajirce kuma kada su sare ko da sun fuskanci wani kalubale a yayin tafiyar su, saboda kalubale abin cin nasara ne, shi nasara ke ci ta tabbata. Su yi iya kokarin su, sannan su bar wa Allah komai.

Shin menene burin ki na gaba a rubutu da ki ke son cimma?

Alhamdulillah ko a yanzu na cika wani bangare na burina a rubutu, sai dai shi buri wani abu ne da yake zaburar da ruhi, idan ka cika wani zuciya za ta sake kyankyasar wani. Haka tafiyar take har iya tsawon rayuwa.

A gaba ina da burin kirkirar wata cibiya ko tsangaya ta marubutan Hausa, wacce zai dinga zakulo musu damarmakin da suka dace da fikirarsu, a ci gaba da damawa da su. Kamar misalin yadda ake samun dama a bangaren cigaban kimiyya da fasaha, inda za ka ga da dama matasa na cin gajiyar abubuwa da suke da kwarewa a kai, a wannan zamani.

Kin tava rubutun waqa ko wasan kwaikwayo irin na fim din Hausa da wasu marubuta ke yi?

Ba na rubuta waqa gaskiya saboda ban iya ba, amma ina sha’awar yi. Haka ban tava rubutun wasan kwaikwayo na Hausa ba, sai dai ina rubutun fassarar finafinan ketare zuwa harshen Hausa.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Mahakurci mawadaci!

Masha Allah. Na gode.

Ni ma na gode kwarai da gaske.