Aljeriya ta kori kocinta bayan cire ta a gasar AFCON

Daga BASHIR ISAH

A ranar Laraba Aljeriya ta kori kocinta, Djamel Belmadi, bayan da aka fitar da ita daga Gasar Cin Kofin Afrika.

Aljeriya ta dauki wannan mataki a kan Belmadi ne bayan da ta sha kashi a hannun Mauritania a ranar Talata a wasansu na karshe na rukuninsu a Ivory Coast.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Aljeriya, Walid Sadi, ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Na hadu da kocin kasar Djamel Belmadi don tattauna abubuwan da ke tattare da wannan rashin nasarar, kuma mun cimma yarjejeniyar kawo karshen dangantakarmu da kuma dakatar da kwantiraginsa.”

Korar Belmadi ta zo ne a ranar da Ivory Coast mai masaukin baki ta kawar da kocinta Jean-Louis Gasset a tsakiyar gasar sannan Ghana ta kori Chris Hughton bayan ficewarta.