Zargin ɓata suna: Kotu ta aike da Ɗanbilki Kwamanda gidan yari a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wata kotu a Kano ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar gidan yari bisa zargin yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a cikin al’umma.

Danbilki dai zai ci gaba gaba da zama a gidan yari har zuwa 29 ga watan Janairu.

Tun da farko rundunar tsaron farin kaya ta DSS ce ta gayyaci Danbilki Kwamanda din wanda tsohon makusanci ne ga tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, kafin daga bisani su gurfanar da shi gaban kotun Majistiri da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.

Sai dai jim kaɗan da tura shi gidan gyaran halin Danbilki Kwamanda ya bayyana cewa gwamnatin Kano ce ta gurfanar da shi ba hukumar DSS ba a shafinsa na Facebook.

Ya ce ” Ba DSS ne suka kaini kotu ba gwamnatin Jihar Kano ce ta kaini kotu, kuma duk abinda aka yi shiryawa a ka yi. DSS sun gayyaceni kuma na amsa gayyata ni ne na kai kaina wurisu sun kuma yi abinda shi ne doka.

“Abinda muke son alƙalai su din ga yi su de na aiki da umarnin wani su yi aiki da doka domin Allah zai tambayesu kowanne hukunci da su ka yi” In ji Danbilki Kwamanda.

Ana tuhumarsa da ɓatawa tsohon gwamnan Kano Senata Rabi’u Musa Kwankwaso suna, kan zargin cewar ya umarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf na yunƙurin rushe masarautun da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirkiro tare kuma da yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a jihar Kano.

Dama Danbarki Kwamanda ya yi ƙaurin suna a caccakar gwamnatin Kano da madugun Jam’iyyar NNPP Dr. Rabi’u Kwankwaso.