Daga BASHIR ISAH
Anayo Nnebe ya rasu ne a ranar Laraba a wani asibitin da aka sakaya sunansa.
Gwamnan Anambra, Chales Soludo ya tabbatar da rasuwar marigayin a wata sanarwa da ya fitar ta bakin Sakataren Yada Labarai, Mr Christian Aburime.
Soludo ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APGA da ma daukacin al’ummar Jihar Anambra.
A halin rayuwarsa, marigayin ya zama Kakakin Majalisar Anambra ne daga 2007 zuwa 2011 inda ya shiga majalisar a matsayin wakilin Awka ta Kudu 1.
Haka nan, an zabe shi a matsayin dan Majalisar Wakilai ta Kasa inda ya wakilci shiyyar Awka ta Arewa tsakanin 2015 zuwa 2019.
