Ndume ya gargaɗi Tinubu kan shirin ɗauke CBN da FAAN zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH

Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar Datawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya gargadi Shugaban Kasa Bola Tinubu game da shirin da yake da shi na mayar da ragamar wasu muhimman bangarorin CBN da kuma Hedikwatar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) zuwa Jihar Legas.

Ndume ya ce muddin hakan ta tabbata, akwai sakamakon da zai biyo baya a siyasance.

Ya ce, “Ba za mu yarda da wannan ba. Hasali ma, ba taimakon Shugaban Kasa suke yi ba, domin kuwa hakan na da sakamako a siyasance”

Sanatan ya yi wadannan kalaman ne yayin wata tattauna da aka yi da shi a tashar Channels TV, inda ya ce wadanda suka ba da wannan bahaguwar shawarar “Lagos boys” ne da ke gwamnatin Tinubu.

Kwanan nan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sanarwa kan matakin da yake shirin dauka na maida wasu muhimman sassan bankin zuwa Legas, yana mai cewa za a yi hakan ne saboda rage cunkoson da sassan ke fuskanta a yanzu.

Kazalika, gwamnati ta bada sanarwar shirinta na dauke babban ofishin hukmar FAAN zuwa Legas don bunkasa harkokinta da kuma rage wa gwamnati kashe kudade.

Sai dai Ndume ya yi ra’ayin cewa in har da gaske ne matsalar cunkoso ce za ta sa a maida ofisoshin da lamarin ya shafa zuwa Legas, da kamata ya yi a mayar da su zuwa jihohi irin su Nasarawa, Kaduna, Kogi da sauran jihohin da ke makwabtaka da Abuja amma ba Legas ba.

“Wasunsun na ganin sun fi kowa sani, sai dai ba su san komai ba. Yayin da ya zamana ba su san Nijeriya ba in ban da Legas, sai su rika yin abu tamkar Nijeriya daidai take da Legas. Legas a cikin Nijeriya take. Wannan ba daidai ba ne,” in ji Ndume.