Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI

A mafi yawan lamura, za ka samu akwai alheri, kuma akan samu akasinsa. Don haka, a irin wannan dambarwar da mafi girman abin da ya jawo ta shi ne rashin kyakkyawan shugabanci, dole sai an yi taka-tsan-tsan. Lallai masu jan ragamar jagorancin al’umma a Najeriya, yawancinsu suna ha’intar al’umma. 

Wani bawan Allah yake cewa da fita ko fecewa daga qasa abu ke mai sauki, to watakila shugabannin kasarmu sai dai su juyo su ga ba kowa, kowa ya kama gabansa. To shi dan’adam da Allah ya yi shi ba ya son a hana shi walwalar abin da yake son aiwartarwa. Don haka, ba za ka hana mutum fita fit, domin ya shaki iskar arziqin da yake ganin ana shaka a wasu wurare ba.

Magana ta gaskiya, ko kasashen da ba su kai Najeriya arzikin ma’adanai ba, irin su Dubai da Qatar da Kanada da Estonia da Bulgaria da Egypt da Malaysia da Singapore da sauransu (duk ana ba mu labarin cewa mun fi wadannan kasashen arzikin wasu abubuwa, amma fa watakila a da), za ka samu a wasu lokutan, sukan fi Najeriya walwalar rayuwa. Don haka dai, ga wasu ‘yan shawarwari kamar haka:

1) Ka kasance mutumin kirki tun a Nijeriyar ma, kafin ma ka yi shirin zuwa wani waje. Ka kasance kana da guzuri na ilimi, ko yaya yake, da tarbiyya da tsoron Allah. In an bar ka a Najeriya kana shashanci, a wata kasar za ka sha mamaki! A nan ai suna sane suke barinmu a shashashai, don su cigaba da yi mana shashatau.

2) Ka nemi sahalewar iyayenka, in suna raye, in ba sa nan, to magabatanka. In iyayenka suka ce ma kar ka je, to kawai ka hakura, kar ka sake ka tafi! Kana ji na? Sai dai za ka iya cigaba da ganar da su a hankali har su fahimta.

3) Ka samu tartibin wajen da za ka je da kuma abin da za ka je yi. Kar ka sake ka hankada kanka zuwa wajen da ba ka san komai game da wajen ba. Za ka iya dacewa, amma fa mafi rinjayen al’amari, shi ne za ka iya tsintar Talatarka a Laraba.

4) Ka tabbatar kana da cikakkun takardu kuma ba na bogi ba. Ana yawan samar da takardun tafiya marasa inganci, ko kuma garin neman ka yi kudi, shi kuma wani ya karve ma naka kudin. Ka ga shi ya yi kudi da kudinka kenan.

5) Ka sani ba ko’ina ba ne ya fi Nijeriya. Kuma wasu kasashen ma in ka je, su ma suna da tasu irin cakwakiyar. Don haka don an ce ma zo ka je Dubai, to fa kar ka zata banza kawai za ka je ka ci. Watakila aikin da ka ki yi a nan, shi za ka je can ka yi, dan bambancin kawai shi ne; can za su biya ka da yawa, kuma ba mai ganin ka.

6) Ba inda ya fi kasarka ‘yanci, kawai rashin kyakkyawan jagoranci ne ya yi mana katutu. Don haka, kar ka zama daga cikin masu aibata kasarka don kai ka tsallake. In an yi sara, a dubi bakin gatari.

7) Kar ka sake ka je inda za ka yi watsi da addininka da al’adunka na gari ka koma dan cuwa-cuwa. Lallai duk abin da za ka yi, ka tabbatar na fafutukar gaskiya ne, ko ba ka samu kudi ba, za ka yi arziki.

8) Kar ka yanke alaqa da dangi bayan ka tafi. In ka yi haka, wata rana za ka iya neman dangin, a lokacin da hakan ba zai amfanar da kai ba.

9) Dogaro ga Allah a duk lokacin da ka yi kyakkyawan shiri, to shi ne a farko da karshe. Kawai ka wuce. Allah ya ba da sa’a.

Muhammad Sulaiman Abdullahi ɗan jarida ne kuma manazarci ne a kan lamurran yau da kullum. Ya rubuto ne daga Beijing ta ƙasar Chana.