Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Daga ZAHRADDEEN IBRAHIM KALLAH

Wato fina-finan Hausa sun yi nisa wajen jan hankalin al’umma. Ko shakka babu wannan dama ce da za a yi amfani da ita wajen sauya tunanin al’umma zuwa ingantatciyar rayuwa da bin dokoki. 

Kwanakin baya a kafofin sada zumunci har majalusu na unguwanni, maganar da na ji ana ta yi ita ce wai raba gardama ya bayyana. Da yake na kwana biyu ba na kallo, na ce wanene wannan raba gardama? Ashe a cikin shirin Labarina ne na Malam Aminu Saira.

A satin nan da muka fita daga shi, sai na ji sabon batu. Ko’ina maganar Al’amin da Maryam ake, wasu na cewa ashe Al’amin babban attajiri ne ya yi vadda bami don ya samu macen da take son sa. 

Wasu kuma ji na yi suna cewa idan suka ga akasin haka, ma’ana marubuci da daraktan shirin sun nuna mafarki ne, ko Al’amin ya sayar da soyayyarsa to sun daina kallon shirin. 

Nan na gyada kai na ce lalle fina-fina Hausa sun fara balaga. Domin wannan zai nuna yadda shirin Labarina ya kama zukatan jama’a. Haka abin yake da shirin Dadin Kowa da Kwana Casa’in tare da Gidan Badamasi.

Amma wataqila mahukunta da masu ruwa da tsaki a cigaban kasa da tattalin arziki ba su fahimci lokaci ya yi da za su shiga harkar fim din Hausa ba don saita tunanin al’umma.
Duk da dimbin masu kallon fina-finan, har yanzu ana kyamar sana’ar ko harkar. Bayan ta zama kusan gidan kowa akwai.

Shekarun baya gwamnatin tarayya ta so ta yi sansanin shirya fina-finai (Film Village) a Kano, amma aka yaki kudirin. Duk da cewa ba a daina fim ba a Kano, kuma masu kallon karuwa suke a sako da loko. 

Sai nake ganin idan da an yi ‘film village’ din, watakila da an killace masu yin fim, tare da tsara musu dokoki bisa al’ada da addini.

Yanzu ba a daina fim din ba. Asali ma kwararo da loko idan ka shiga, za ka tarar ana daukar fim, inda za ka ga yara sun taru ana kallon taurarin fim duk da yadda wasunsu ke varin zance da mugun wasa.

Fitaccen shirin Dadin Kowa ana shirya wani bangare a Kawo dake garin Kano. Kwanaki can ina kallo shirin, sai na ga an nuno wani gida da wasu taurarin shirin suka yi aure a ciki. Koda aka shiga falon, nan na tabbatar dakin kanwar mahaifiyata ne.

Wannan zai nuna cewa shirin ya shiga jama’a sosai. Shirin ya zama wani bangare na rayuwarsu. Idan da wani abin ki, to an gudu ba a tsira ba. Tun da ba ta sake zani ba.

Shirin fim ba mai gushewa ba ne nan kusa. Ya kamata a karbe shi hannu bibiyu tare da tunanin yadda zai amfani jama’a ta hanyar da ta dace.

Zaharaddeen Ibrahim Kallah marubuci ne kum amai sharhi a kan lamurran yua da gobe. Ya rubuto daga jihar Kano