Allah ya jiƙan ɗan Amanar Abacha

Daga MAHADI M. MUHAMMAD

Na karanta tarihin ‘yan gwagwarmayya da yawa, amma ban tava ganin mai akida da amana irinta Wada Nas (Dan Amanar Abacha) ba. Sunansa na gaskiya Muhammad Hamisu.

An haife shi a unguwar Nasarawa da ke Funtua ta yanzu a shekarar 1938. Shi ne dan auta a wajen iyayensa. Ana yi masa lakabi da Wada ne saboda wadatar raguna da aka samu a ranar radin sunansa. Mahaifinsa ya tanadi ragon suna guda daya, Sarkin Katsina na wannan lokacin ya aiko da rago daya. Wazirin Katsina kuma ya aiko da raguna biyu. Wannan ya sa ake masa lakabi da Wada. Yana d’an shekaru biyu mahaifinsa ya rasu. Bayan ya kai shekaru shida mahaifiyarsa ta rasu. Wannan ya sa Yayansa Alhaji Garba Nasarawa ya dauke shi ya rike shi.

Ya yi makarantar Elementary ta Funtua daga shekarar 1945 zuwa 1949. A nan ne ya sauya sunansa daga Wada Nasarawa zuwa Wada Nas. Ya shiga Kwalejin Katsina a shekarar 1952 ya gama 1954. Daga nan ya wuce Kwalejin horas da Malamai ta Katsina a shekarar 1955. A nan ne ya fara sha’awarar siyasa har ya rubutawa shugaban jam’iyyar NEPU ta ƙasa (wato Malam Aminu Kano) wasikar neman shiga jam’iyyar.

Amma sai Malam Aminu Kano ya basa shawarar ya kammala makaranta tukun, domin siyasa tana bukatar masu ilimi irinsa. Bayan ya kammala karatu ya samu aikin koyarwa a Katsina, sai ya tsunduma jam’iyyar NEPU.

Wada ya fuskaci tsangwama daga Masarautar Katsina saboda yadda Masarautar ta tsani jam’iyyar NEPU.

Wannan ya sa Sarkin Katsina ya sa aka yi masa sauyin wajen aiki zuwa karamar hukumar Kaita. A nan ma ba ta sake zani ba, domin Hakimin Kaita ya haramta dukan wani abu da ya shafi jam’iyyar NEPU. Amma da Wada ya je, sai ya fara gudanar da harkokinta tare da yada manufofinta.

Da Hakimin ya hanasa ya ki hanuwa, sai ya sa jama’ar garin su daina yi masa magana kwata-kwata. Haka kuwa aka yi, hatta a kasuwa idan Wada ya je sayan abu ba a sayar masa, sai dai yaje Katsina ya saya. Direbobin motan da za su dauke shi zuwa Katsina su ma suka qi xaukarsa. Masu Keke suka qi basa haya. Da qafa yake tafiya tun daga Kaita har Katsina ya yi sayayya ya dawo.

A shekarar 1959 Malam Aminu Kano ya tsayar da shi takarar dan majalisa tarayya mai wakiltar Kankara da Kogo. Cikin nufin Allah ya ci zabe. Da jam’iyyarsu ta qauracewa zaben 1964, sai ya dawo gida ya ci gaba da harkar noma.

Bayan juyin mulkin farko dana biyu ya samu aiki a matsayin Akawu (accountant) a ofishin cinikin amfanin gona ta Arewacin Nijeriya. A jamhuriyya ta biyu kuma ya shiga jam’iyyar NPN ya zama kansilar lafiya na Funtua kafin daga baya ya zama sakatare a tsohuwar jam’iyyar jihar Kaduna daga shekarar 1981 zuwa 1983. A jamhuriyya ta uku ya koma jam’iyyar NRC ya zama shugabanta na jihar Katsina.

A karkashin shugabancinsa dan takarar jam’iyyar, wato Alhaji Sa’idu Barde ya kayar da dan takarar jam’iyyar SDP Alhaji Umaru Musa ‘Yar’adu a zaben gwamnan Katsina na farko. Bayan juyin mulkin 1993, shugaban mulkin Soja Janar Sani Abacha ya nada shi karamin ministan ilimi. Wada Nas yana matsayin minista amma ya fi mayar da hankali wajen kare gwamnati daga sukar ‘yan adawa musamman magoya bayan Abiola. Ganin haka ya sa Abacha ya sauya masa mukami zuwa ministan ayyuka na musamman.

Daga baya kuma ya zama mashahurci na musamman akan ayyuka har zuwa lokacin da Allah Ya yi wa Abacha rasuwa. Hatta bayan mutuwar Abacha, Wada bai daina kare gwamnatin Abacha ba. Musamman lokacin da wasu magoya bayan Abacha suka koma sukarsa bayan ba ransa. Wannan ya sa ake masa lakabi da ‘Dan Amanar Abacha’. Bayan dawowar mulki hannun farar hula, sai ya zabi ya koma gefe ya zama dan kallo.

A lokacin ne ya shiga bayyana ra’ayoyinsa a jaridar Wekkly Trust, inda jama’ar da a baya suke zaginsa suka dawo yabonsa saboda caccakar gwamnatin Obasanjo da yake yi. Ganin yadda gwamnatin Obasanjo take tafiyar da mulkinta ya sa ya sake dawowa siyasa ya shiga jam’iyyar APP wadda ta zama ANPP daga baya. Dan Amanar Abacha yana cikin mutanen da suka jawo Buhari ya shiga siyasa.

Allah Ya yi masa rasuwa a ranar 3 ga watan Janairun 2005 a asibitin Kwararru na Al’mansur da ke Kaduna baya ya sha fama da rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 66; ya bar mata 2 da ‘ya’ya 20 da kuma jikoki.

Mohammed Bala Garba, Maduguri.
7 ga watan Junairun 2024.