Basaja a zaman aure (1)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma’aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi kamari ya kai ga rusa auren gabadaya.

To wai meye basaja?

Na san mai karatu zai so ya san ma’anar basaja. Basaja kamar sani azancin maganar nan ne da ake cewa kitsen rogo. Wannan azancin na nufin kamar yadda muka sani rogo yana da fari, musamman danyensa idan aka bare shi. Daga nesa za ka gan shi fari sol har daukar ido yake yana wani maiko kamar dai kitse yake. Amma daga ka matso kusa, sai zance ya sha ban-ban domin za a ganshi a bushe kuma ba zai kai darajar da ake tsammanin yana da ita ba a lokacin da ake hangensa daga nesa. To haka ma rayuwar aure a kasar Hausa.

Wato dai yanke hukunci da hange a zamantakewa ba tare da zurfafa bincike ba.

A kasar Hausa wani lokacin dalilai da yawa da suke jawo mutuwar aure shi ne yi wa aure kallon kitsen rogo. An kasa gane shi aure wani zama ne da ake fatan mutu-ka-raba wato da’iman. Daukar aure akasin haka, matsala ce babba wacce za ta sa ya yi karkon kifi.

Da farko ba a shiga aure da gaskiya sai don hangen wani abu wanda ba shi ba ne. Mutane da yawa suna shiga gidan aure da nufin shakatawa da watayawa. An manta aure gidan bautar Allah ne.

Kuma ita bautar Allah ba abu ce mai sauki ba. Eh an san ba wanda yake fatan ya samu matsala a gidan aure. Amma kuma ita matsala dole ce. Bahaushe ya ce: “zo mu zauna, zo mu sava”. Amma wasu sukan shiga aure da wannan zaton saboda yadda abokin rayuwar tasu ya dora su a keken vera ko igiyar zato.

Misali kamar wasu mutanen idan an zo maganar aure sukan yi wa wanda za su aura wata karya har a dora shi a igiyar zato. Kamar maza sukan kwadaita wa mata wata rayuwa da ka san ba za ta dore ba. Ita kuma sai ta yaudaru da wannan abun, ta aure shi. Tana ganin mai dorewa ne. Haka wasu mazan a satittikan farko na aurensu sukan tarairayi mace su sangarta ta ko cimaka ma sukan ba ta wacce suka san za ta birge ta. Ita kuma sai ta afka cikin tarkon, ta yaudaru ta dinga ganin za a dore. Daga lokacin da abubuwa suka, canza sai rigima ta faru. Idan ba a ci sa’a ba auren ma ya ruguje.

Akwai kuma wani kallon kitsen a rogo da ma’aurata kan yi a kan rayuwar wasu ma’auratan. Wanda rashin godiyar Allah ne yake jawo hakan. Wasu ma’auratan sukan dinga hangen rayuwar wasu har ma su dinga shauqin ina ma su ne. Har ma su dinga ta da wa abokan rayuwarsu da hankali a yi ta rigima kala-kala har ma a rusa auratayya.

Wasu ma fa kawai rayuwar da suke gani a akwatinan talabijin dinsu ko a littattafan kagaggun labarai da suke karantawa. Sai a rude a raina kokarin wanda ake tare da shi.

An san cewa ana koyon wasu abubuwa na rayuwa da kuma zamantakewa a sashen adabi amma a sani, wasa daban rayuwar zahiri daban. Mata su suka fi yin wannan. Musamman masu kananan shekaru. Daga zarar mijinta ba ya yi mata irin rayuwar da ta ga mijin wata kawarta ya yana yi mata, ko yadda ta ga tauraron wani fim ko kagaggen labari yana wa matarsa ba, to za dinga ganin kamar ba sonta yake ba.

Haka shi ma namiji yana ruduwa da cika bakin abokanensa ko ‘yanuwansu maza. Su dinga cika bakin yadda suke tafiyar da rayuwar gidansu da yadda suke daure wa matarsa ko matansa fuska da sauransu. Kai kuma sai ka yi sha’awa ka gwada a kan baiwar Allar matarka.

Haka su ma mata akwai kawaye da za su dinga cika muku baki mijinta ya yi mata kaza da kaza. Ya kashe mata kudade kaza-kaza. Ko kuma ta dinga nuna irin yadda ta mallake shi yake mata biyayya da sauransu. Ko yadda take dila kishiya ko ‘ya’yan miji ke kuma ki yi sha’awa ki gwada a naki gidan kwavarki ta yi ruwa. Ki rusa aurenki idan ba ki yi sa’a ba.

Ko kuma ki hango ko ki ji labarin wata a wani tamfatsetsen gida ga motoci, ga daula. Ki dinga hangen ke ba ki yi sa’a ba, ki fitini kanki a banza. Wata ma sai ta kashe aurenta saboda wancan hange da take yi ya sa har ta dinga raina mijinta da dukkan samunsa da abubuwan da yake yi mata na kyautatawa.

Amma abinda muka kasa ganewa shi ne, shi fa rogo, rogo ne. Kitse ma, kitse ne. Duk yadda ya yi maka kyau daga nesa, sai ya ba da kai idan ka matso kusa. Don haka mu daina yaudaruwa da kallon kitse a matsayin rogo.

Sannann mun kasa gane cewa shi kowanne miji ko mata da irinsa. Kowanne mutum bai cika goma ba. Duk yadda abokin rayuwarku yake dan Adam ne. Dole akwai inda ya gaza komai kokarinsa. Ku daina hangen rayuwar wasu. Su ma yadda kuke sha’awarsu haka watakila suke ganin kamar ku ma ba ku da matsala.

Kuma kowanne dan Adam da tasa jarrabawar. Misali kamar matar nan da kuka gani tana fantamawa a cikin daular makeken gidan nan. Allah ne kadai ya san wacce jarrabawa Allah ya dora mata. Wataqila akwai matsalar dangi ko na uwar miji da ba sa kaunarta, ko kangararren da, ko rashin adalcin miji da sauransu. Amma ke ba ki yi tunanin komai ba sai daular da take ciki. To ki bude idanunki ki gane, wancan kitsen da kike hangowa mai yiwuwa rogo ne. Rogon ma busasshe mai daci.

Haka wasu ma za su iya yi muku karya su nuna muku sam ba su da matsala. Kamar wancan mijin da na kawo misalinsa a sama wanda yake cika baki a kan yadda yake dila iyalansa. Watakila ma fa duk bula ce. Watakila a gidan ma ba shi da katavus. Amma ya cika muku baki ya dora ku a keken vera kuna neman rusa aurenku.

Haka ma mata, musamman masu sayar da kayan mata kan kuranta cewa, mazansu a tafin hannunsu suke. Ke kuma ki je ki yi ta wahalar da kanki sai mijinki ya zama haka. Daga karshe ki tuge igiyar auren naki gabadaya. Hattara da kallon kitse a matsayin rogo.

Za mu cigaba mako mai zuwa idan Mai duka ya kai rai.