Shin a Nijeriya ma ana yin digirin siyarwa?

Daga MUSA AYUBA IBRAHIM

Akwai wani da ya nuna min wani babban ma’aikacin gwamnati ya ce: su na shekararsu ta karshe suka fara ganin sa, yana shigowa jifa-Jifa lakca ya zo su gaisa, bayan gama jami’ar sai ga sunan sa a jerin waɗanda suka kammala digiri. Ba su san shi ba tun daga farko sai shekarar karshe a zango karshe.

Wani dan uwa na an tava masa tallan Irin wannna digirin a wata jami’a a kan wani i adadin kudi amma na bashi shawarar hakura gaskiya duk da har samfuri sun nuna masa da misalan mutanen da aka musu.

Saboda haka kes din dai kawai:

Wanda ya sani ya sani ne, in bai zo ta wurinka ba ba za ka gane ba. Su kuma wadannan jami’oin na ketare ba wai Kwatano (Coutonou) kadai ba, a tsarin karatu kan su, ko wanda suke yi da gasken ma, ba wani abu ne mai tsauri da fita hayyaci irin yadda muke yi a Nijeriya ba.

Ba su dauki digiri din irin yadda muka dauka ba, da za ka shafe kusan shekaru 5 zuwa shida ka na yi ba.

Komai da sauki ba tsauwala wa mai kyau da Ingancin ma a wuraren su ba ya wuce shekara 2 ma gabadaya.

Daga shafin Muhammad Mahmud na dandalin Fesbuk