Da Ɗumi-ɗumi: EFCC za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Anambra, Obiano kan badaƙalar N4bn

Daga BASHIR ISAH

Ya zuwa ranar Laraba ta wannan makon ake sa ran Hukumar Yaki da Rasha (EFCC) za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun da ke Abuja, kan zargin wawushe kudaden gwamnati da ya kai Naira biliyan 4,008,573,350 kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta rawito.

Jairdar ta ce za a gurfanar da tsohon gwamnan ne kan zargin laifuka guda tara.

Wannan na zuwa ne bayan da Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya lashi takobin sake waiwayar kesakesan da suka shafi shafaffu da mai, musamman tsoffin gwamnoni da ministoci.

Majiya mai tushe ta ce, “Mun gano cewa Obiano hankada N4,008,573,350 daga kudaden tsaron jihar zuwa asusu daban-daban. Kuma an canza kudaden a lokuta mabambanta zuwa Dala sannan aka maida wa Obiano da tsabar kudi.”

Jagoran tawagar lauyoyin EFCC, Slyvanus Tahir, SAN, shi ne zai jagoranci sauran lauyoyi takwas wajen gurfanar da tsohon gwamnan.

Obiano ya yi Gwamnan Anambra ne daga shekarar 2014 zuwa 2022 inda ya mulki jihar na wa’adi biyu.