Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Nijeriya ta sha alwashin bibiyar hakkokin Arewacin Nijeriya da ake kokarin karkatarwa.
Kakakin kungiyar kuma Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai.
Kungiyar Sanatocin na bayyana hakan ne a lokacin da take maida martani dangane da wasu matakai da Gwamnatin Tarayya ta dauka na ba wa Kudancin Nijeriya fifiko a kan wasu abubuwa da suke hakkin kasar ne gaba daya.
Kuma batutuwan da suka yi martanin a kansu sun hadar da ba wa Kudancin Nijeriya fifiko a kan kasafin kudin shekarar 2024, dauke shalkwatar Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN), dama dauke wasu manyan ofisoshin Babban Bankin Kasa (CBN) daga Abuja zuwa Legas.
Kungiyar ta ce ta karbi korafin al’ummar Arewa ta fannoni da dama, don haka ta ce ya zama wajibi ta bibiyi lamarin domin tabbatar da cewa matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka ba su cutar da Arewacin Nijeriya ba.
Sumaila ya kara da cewa, kungiyar za ta hada hannu da dukkan bangarorin da ya kamata domin ganin an kwato wa Arewacin Nijeriya hakkinsu, kamar yadda dokar kasa ta tsara.
Sannan kungiyar ta bukaci mutanen Arewacin Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, domin a bi batun ta hanyar maslaha ko kuma ta hanyar daukar mataki na shari’a.
