Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Tsohon Ministan Tsaron Nijeriya, Alhaji Lawan Ɓatagarawa, ya bayyana cewa kwace makamai daga hannun masu aikata laifuka ne mafita mafi inganci wajen magance matsalar rashin tsaro, ba sulhu da su ba.
Ɓatagarawa ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wani taro na ƙungiyar ‘yan kasuwar sayar da kayan abinci a buhu, wanda aka gudanar a zauren taro na Mumbayya, cibiyar tunawa da marigayi Malam Aminu Kano da ke unguwar Gwammaja a Kano, a makon da ya gabata.
Ya ce sulhu da ‘yan ta’adda na iya zama tamkar mika wuya ne ga masu aikata laifuka, musamman la’akari da yadda suke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, musamman a Arewacin Nijeriya.
Tsohon Ministan ya jaddada cewa ba za a iya samun cigaban tattalin arziki ba tare da tsaro ba. Ya ce dole ne shugabannin ƙasa a dukkan matakai su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin Nijeriya.
Batagarawa ya kuma bayyana cewa matsalar tsaro ta yi tasiri sosai ga harkar noma, wanda hakan ya haifar da tsadar kayan abinci da kuma raguwar samar da amfanin gona. Ya ce duk da sauƙin farashin abinci da ake samu a halin yanzu, akwai buƙatar samar da tsari mai ɗorewa domin bunƙasa harkar noma a ƙasar.
Hakazalika, ya yaba wa ƙungiyar Rains Marketers Association of Northern Nigeria, ƙarƙashin jagorancin shugabanta na Kano, Alhaji Abba Mustapha Ungogo, da shugabanta na Arewacin Nijeriya, Alhaji Mustapha Inuwa Mai Hatsi, kan shirya taron da aka tattauna batutuwan shugabanci, siyasa da tattalin arziki.
Taron ya samu halartar malamai, masana, ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa daga sassa daban-daban. Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai ta Arewa, wanda ya samu wakilci, sai Farfesa Usman Sani Abbas, Dakta Nura Abdullahi wanda ya wakilci Farfesa Yahuza Bello, da Dakta Saidu Ahmad Dukawa, tare da fitaccen ɗan jarida Malam Bashir Bashir.
Sauran mahalarta sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Kano, Alhaji Musa Ungogo, da wasu manyan baki, waɗanda suka gabatar da jawaban da suka shafi matsalolin Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
A ƙarshe, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Mustapha Ungogo, ya nuna gamsuwa da haɗin kai da gudunmawar da mahalarta taron suka bayar, tare da bayyana cewa tattaunawar da aka yi za ta taimaka wajen nemo hanyoyin warware matsalolin da ke addabar yankin Arewa.
