Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa ya naɗa hakimai 28 a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa, Gwani Malam Salisu Liman, ya naɗa hakimai guda 28 domin faɗaɗa masarautarsa tare da inganta zaman lafiya, fahimtar juna da haɗin kan al’umma a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

An rawaito cewa naɗin hakiman ya biyo bayan naɗin da Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar, ya yi wa Gwani Malam Salisu Liman a matsayin Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa a Nijeriya.

Da yake jawabi yayin bikin naɗin hakiman a ƙarshen makon da ya gabata, Sarkin ya ja hankalin sabbin hakiman da su yi aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan jama’a, tare da girmama matsayin da aka ba su. Ya ce sarauta baiwa ce daga Allah, don haka wajibi ne masu riƙe da ita su yi amfani da ita wajen taimakawa al’umma.

Daga cikin hakiman da aka naɗa akwai Gwani Muhuyideen, Wazirin Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa, da Shehu Mustapha Danladi Aminu, sai Gwani Yahuza Muhammad Jajaye, Hakimin Laƙanin Sarkin ƙasar Hausa na Rogo. Haka kuma akwai Sarkin Ban, Matawallen Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa, da Hakimin Laƙanin ƙasar Hausa na Sumaila, Malam Hamza Muhammad Magani.

Sauran sun haɗa da Malama Khadija Inuwa Nasir, wadda aka naɗa a matsayin Hasken Fadar Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa, da kuma Malam Muhammad Mustapha, Hakimin Laƙanin Sarkin ƙasar Hausa na ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, tare da sauran hakimai da dama.

Hakiman da aka naɗa sun yi jawaban godiya tare da yabawa Sarkin Laƙanin ƙasar Hausa bisa amincewar da ya yi da su, inda suka yi alƙawarin yin aiki domin ci gaban al’umma.

Majiyoyi sun bayyana cewa yawancin waɗanda aka naɗa malamai ne kuma hafizan Alƙur’ani, waɗanda suka shahara wajen koyar da ilimi da bayar da gudunmawa ga cigaban addini da zamantakewar al’umma.

By ukarofi