Rundunar ‘ƴan sandan Jihar Kaduna sun hana duk wani taro da Yan Shi’a ke shirin gudanarwa a ranar Ashura.
Mai magana da yawun rundunar na Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ne bayyana haka a wani sanarwa a ranar Lahadi, a kaduna.
Yace rundunar ta sami bayanan sirri da ke nuni da cewa Ƙungiyar Ƴan Shi’a za su gudanar da tattaki ranar Ashura. Wanda yace tattaki fa suka yi a baya baya ya haɗu da tashin hankali, da asarar dukiya da rayuka.
Ya ƙara da cewa rundunar ba za tai ƙasa a gwiwa ba don ganin doka tayi aiki kan duk wanda ya ƙarya ta.
Daga ƙarshe yace, kwamishinan ƴan sandan Jihar Kaduna, Mr Ali Dabigi, yayi kira ga dukkan mutane su zama masu bin doka da oda.
