Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da kafa Ma’aikatar Kiwon Dabbobi ta Tarayya a wani mataki da ake sa ran zai kawo ƙarshen rikicin makiyaya da manoma.
Tinubu ya amince da kafa ma’aikatar ne a ranar Talata a lokacin da ya ƙaddamar da kwamitin shugaban ƙasa kan sake fasalin kiwon dabbobi a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja.
Nijeriya dai ta shafe shekaru da dama tana fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya. Amma Tinubu ya tabbatar da cewa yana da yaƙinin samar da ma’aikatar zai warware matsalar da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.
“Waye ya ce mafita ta yi nisa? Na ce, ‘A’a, mafita tana nan kusa.’ Yawancin ku kuna da ƙwarewa sosai kuma kuna son Nijeriya ta ci gaba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa “Don baiwa Nijeriya damar samun cin moriyar noman dabbobi, mun ga mafita da kuma damar da za a magance wannan bala’in da ya addabe mu tsawon shekaru kuma na yi imanin cewa muna daf da samun wadata.”
A yayin da shugaba Tinubu zai jagoranci kwamitin sake fasalin kiwon dabbobin, tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Attahiru Jega, shi zai kasance mataimakinsa.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari da nufin samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma, da tabbatar da tsaro tare da bunƙasa tattalin arzikin ’yan Nijeriya.
