Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewar ‘yan Nijeriya miliyan 82, kimanin kashi 64 na ‘yan ƙasar, ka iya fuskantar matsalar matsananciyar yunwa nan da shekarar 2030.
Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce alƙaluma daga binciken shekara-shekara kan abinci sun nuna cewa nan da shekaru masu zuwa lamurra za su ta’azzara a ƙasar.
Haka kuma MDD ta yi kira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ƙwari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana.
A wurin wani taron kan haɓaka ayyukan noma a Abuja ne jami’in Majalisar, Taofiƙ Braimoh ya bayyana cewa, “Gwamnatin Nijeriya tare da haɗin gwiwa masu ruwa da tsaki, sun gudanar da bincike na shekara-shekara da suka saba gudanarwa kan abinci. Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kimanin mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030.’
Ya ci gaba da cew matsalar rashin abinci da ƙasar ke fama da shi, baya rasa nasaba da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, da matsalar ƙwari da wasu abubuwa da ke yi wa harkar noma tarnaki a ƙasar.
Hasashen na Majalisar Ɗinkin Duniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsadar abinci, lamarin da ya tilasta wa gidaje da dama haƙura da sayen abincin da suka saba ci.
A cikin rahotonta baya-bayan nan, hukumar ƙididdigar ƙasar ta ce farashin abinci a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 40.66 a watan Mayu, matakin da aka jima ba a ga irinsa ba.
A shekarar da ta gabata ne dai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan abin, a wani mataki na yunƙurin wadata ƙasar da abinci.
A baya-bayan nan ne gwamnatin Nijeriya ta sanar da wasu matakai don kawo sauƙi ga halin matsi da al’ummar ƙasar suke ciki.
Ɗaya daga cikin matakan shi ne, gwamnatin za ta fito da tan 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma da nufin kawo sauki ga halin matsin rayuwa da al’ummar ƙasar ke fama.
Sannan gwamnatin ta ce ta tattauna da masu kamfanonin sarrafa shinkafa a faɗin Nijeriya inda suka amince su fito da tan 60,000 domin sayar wa al’umma faɗin ƙasa.
