Ƴar Galadiman Dutse mai shekaru 62 ta rasu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Iyalan gidan Galadiman Dutse, Alhaji Basiru Muhammad Sanunsi na cikin alhini, biyo bayan rasuwar ɗaya daga cikin ƴaƴansu mai suna Hafsatu Basiru Sanusi.

Marigayiyar wacce aka haifa a ranar 31 ga watan Mayu, 1962, ta bar ƴaƴa huɗu cikin har da Lukman Mahmoud Isa Dutse, ma’aikacin bankin CBN reshen Abuja, da kuma Alawiyyah Mahmoud Isa Dutse, ma’aikaciyar kamfanin inshora na ƙasa (NDIC) dake Abuja.

Wasu daga cikin ƴan uwanta sun haɗa da; Jamilu Basiru Sanusi, Turakin Dutse da Zahraddeen Basiru Sanusi, Dan Isan Dutse, da kuma Sanusi Basiru Sanusi, Ɗan Darman Dutse.

Hafsatu ta kasance jigo ce a cikin iyalanta ganin yadda take taimaka wa gidan ta fuskoki da dama wanda hakan ya sa za a yi matuƙar kewarta, sannan kuma saboda halinta na kirki ake fatan ta zama abun kwaikwayo ga ƴan baya.

Allah Ya jiƙan ta Ya kuma gafarta mata, Amin.

By Babaji