Hukumar Kwastom ta kama katan 2625 na kodin da kuma katan 80 na sildenafil. Kwanturola na Area 11 command da ke Onne jihar Ribas ne ya nuna wa manema labarai waɗannan kayan. Aƙalla kayan zasu yi naira 2, 250,654,000.
Yace waɗannan kayan suna da illa sosai ga lafiyar mutane. Ya ƙara da cewa wannan aikin haɗin gwiwa ne tsakanin kwastom da hukumar hana safara da shan miyagun ƙwayoyi.
Yace waɗannan abubuwan shigo dasu ya saɓawa dokar da ƙasa ta tanada na shigowa da abubuwa daga wani wuri. Ya rufe da yin godiya ga hukumar hana sha da safara miyagun ƙwayoyi wanda da taimakonsu aka samu wannan nasarar.
