Daga MAHD MM. MUHAMMAD
Wata Kotun Majistare da ke Abeokuta, reshen Isabo, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wata mata ’yar shekara 25 bisa zargin ta da yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 mummunar azaba da wuta ta hanyar ɗaɗara mata a al’aurarta.
Wadda ake tuhumar wadda ke zaune a lamba 6 Isewo Dotin a unguwar Obada-Oko a Abeokuta, tana fuskantar tuhuma guda ɗaya da laifin haddasa mummunar ɓarna.
Wadda ake tuhumar ta amsa laifin da ake tuhumarta da aikatawa tare da roƙon gafarar kotun.
Alƙalin kotun, B.Ɓ. William, ta bada umarnin tsare ta a gidan gyaran hali sannan kuma ta buƙaci masu gabatar da ƙara da su kwafe tare da aika fayil ɗin ƙarar zuwa ga Daraktan ƙararrakin jama’a domin samun shawarar shari’a.
William ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 26 ga watan Yuni domin ambato.
Tun da farko, lauya mai shigar da ƙara, Lawrence Olu-Balogun, ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Yuni a lamba 6, Isewo Dotin, a unguwar Obada.
Ya yi zargin cewa wadda ake ƙara, kasancewarta mariƙiyar wadda abin ya shafa, ta saka itace mai ci da wuta a al’aurar yarinyar bisa zargin satar kayan sha da aka kiyasta kuɗin su ya kai Naira 650.
Ya shaida wa kotun cewa laifin ya ci karo da sashe na 316 da 319 na kundin dokokin jihar Ogun na shekarar 2006.
