Ɗan Ganduje ya koma NDC, ya yanki tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya yankin tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin tutar jam’iyyar NDC.

Rahotanni sun bayyana cewa, Abdulaziz ya yanki fom ɗin ne a yau Asabar domin shiga takarar ta mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a zaɓen 2027 da ke tafe.

Wannan mataki ya janyo cece-kuce a fagen siyasa da alaƙar Abdulaziz da tafiyar Kwankwasiyya na tsawon lokaci duk da tasirin mahaifinsa a APC a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

Ana ganin Abdulaziz a matsayin mai biyayya ga Rabi’u Musa Kwankwaso kuma ya jima yana cikin tafiyar Kwankwasiyya a shekaru da dama.

Haka kuma, an ga yadda Abdulaziz da Kwankwaso suke ganawa a wani faifan bidiyo jim-kaɗan bayan mallakar fom ɗin, inda ya shaida wa jagoran Kwankwasiyyar muradinsa na siyasa da shirinsa na shiga takara a babban zaɓen.

By Babaji